Obasanjo na kokarin ganin kasar Amurka ta sauke takunkumin da ta sa wa Atiku - APC

Obasanjo na kokarin ganin kasar Amurka ta sauke takunkumin da ta sa wa Atiku - APC

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki tayi zargin cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo na yunkurin sama wa dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar visan shiga kasar Amurka.

A wata sanarwa dauke da sa hannun Yekini Nabena, mukaddashin kakakin jam’iyyar yace Obasanjo na roko hukumomin US das u janye takunkumin hana shiga da aka sanyawa Atiku bayan zargin karban cin hancin $500,000 a 2005 wanda ya hada da matar Atiku ta hudum Jennifer, da tsohon jami’in Amurka, William Jefferson.

Obasanjo na kokarin ganin kasar Amurka ta sauke takunkumin da ta sa wa Atiku - APC

Obasanjo na kokarin ganin kasar Amurka ta sauke takunkumin da ta sa wa Atiku - APC
Source: Facebook

Jam’iyyar ta ci gaba da cewa sanya baki da Obasanjo yayi wajen ganinan dage wa Atiku haramcin shiga Amurka hujja ce na cewa yana da son zuciyarsa a cikin lamuran kasar.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto cewa babban malamin nan na Musulunci, Sheikh Ahmed Gumi ya bayyana dalilinsa na zuwa wajen sulhunta tsakanin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo da tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.

KU KARANTA KUMA: Ina fuskantar matsin lamba kan barin APC - Yari

A cewarsa yayi koyi ne da annabi Muhammad, domin cewa ko a zamaninsa ya halarci sulhu a tsakanin yahudawa don wanzar da zaman lafiya.

Gumi yace shugabannin biyu ne suka bukaci a gayyaci wanda babu ruwan shi da bangaranci, don haka aka zabo shi saboda shi babu ruwan shi da wani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel