Bututun mai ya fashe a Abia, mutane 19 sun mutu a sanadiyyar gobarar

Bututun mai ya fashe a Abia, mutane 19 sun mutu a sanadiyyar gobarar

Kimanin mutane goma sha tara ne suka rasa rayukansu yayin da wasu bututun mai suka farfashe a wasu kauyuka biyu na cikin karamar hukumar Osisioma dake jahar Abia, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamandan rundunar tsaron farin kaya ta civil defence na jahar, Benito Eze ne ya bayyana haka a ranar Juma’a 12 ga watan Oktoba a yayin ganwarsa da manema labaru a garin Umuahia.

KU KARANTA: Farawa da iyawa: Cacar baki da nuna ma juna yatsa ya kaure tsakanin yan takarar shugaban kasa

Kwamanda Eze yace mutane sha shida suka mutu a gobarar da ta biyo fashewa bututun mai a kauyen Umuaduru dake cikin garin Umueze da misalin karfe 2:47 na dare, daga cikin su har da wata mace guda daya.

Haka zalika wasu mutane uku sun mutu sakamakon gobarar da ta biyo kamawa da wuta da jarkokin mai suka yi da misalin karfe 3 nadare a kauyen Umuimo, kamar yadda Eze ya bayyana, inda yace da misalin karfe hudu na dare ya isa kauyukan.

Sai dai kwamandan ya danganta gobarar Umuaduru ga rashin hankalin wasu matasa dake kwasar mai daga bututun da suka fasa: “Na samu labarin matasan kauyen ne suka fasa bututun mai suna diban mai, daga nan ne aka samu dan tashin wuta, wanda ya yi sanadiyyar gobarar da ta kasha mutane 16 nan take.

“Shi kuma gobaran Umuimo ya faru ne a lokacin da wata mata ta tashi da misalin karfe uku na dare da nufin za ta yi girki, ashe sun tara man fetir a gidannasu, kyasta ashananta keda wuya, sai jarkokin man suka kama da wuta, inda ya kashe mutane uku amma matar da mijinta basu mutu ba.”

Sai dai majiyar Legit.ng ta ruwaito akwai wasu jami’an Sojoji guda uku da suka mutu a sakamakon gobarar, amma kwamanda Eze bai tabbatar da labarin ba, inda yace sai sun kammala bincike zasu tabbatar da haka ko akasin haka.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel