Ina fuskantar matsin lamba kan barin APC - Yari

Ina fuskantar matsin lamba kan barin APC - Yari

Gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari a ranar Juma’a, 12 ga watan Oktoba ya bayyana cewa yana fuskantar matsin lamba daga magoya bayansa kan ya sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Yari wanda ya kasance shugaban kun giyar gwamnonin Najeriya yayi Magana da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan ganawarsa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ya kuma mika sakamakon zaben fidda gwani da aka gudanar a jihar ga shugaban kasar bayan sallar Juma’a.

Ina fuskantar matsin lamba kan barin APC - Yari

Ina fuskantar matsin lamba kan barin APC - Yari
Source: Depositphotos

Yayi alkawarin cewa duk da matsin da yake fuskanta daga mutanensa na ya bar APC, zai ci gaba da kasancewa a jam’iyyar sannan ya yaki rashin adalci.

KU KARANTA KUMA: NEMA ta bayyana jerin wasu jihoh da za su sake fuskantar ambaliyar ruwa

A cewarsa, magoya bayansa sun fusata kan yadda abubuwa suka koma bayan shugaban jam’iyyar ya gaaza yin Magana akan zaben fidda gwanin da aka gudanar a makon da ya gabata a jihar.

Yace lamarin yasa magoya bayansa sun gaji.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel