NEMA ta bayyana jerin wasu jihoh da za su sake fuskantar ambaliyar ruwa

NEMA ta bayyana jerin wasu jihoh da za su sake fuskantar ambaliyar ruwa

A kokari da ake na ganin an magance matsalar ambaliyar ruwa a kasar, hukumar bayar da agajin gaggawa na kasa (NEMA) ta kaddamar da cewa annobar ambaliyar ruwa zai afku a wasu jihohi biyar.

Ku tuna cewa a ranar 17 ga watan Satumba, hukumar ta kaddamar da jihohi biyar da suka hada da Niger, Kogi, Anambra da Delta a matsayin jihohin da ambaliyar ruwa zai afku, jaridar This Day ta ruwaito.

A yanzu kuma an sake ambaton jihohi biyar da za su fuskanci haka, jihohin sune , Taraba, Rivers, Kebbi a Bayelsa, hakan yasa su jihohin sun koma tara, inda tsoro ya darsu a zukatan jihohin dake a lissafin hukumar NEMA.

NEMA ta bayyana jerin wasu jihoh da za su sake fuskantar ambaliyar ruwa

NEMA ta bayyana jerin wasu jihoh da za su sake fuskantar ambaliyar ruwa
Source: Facebook

Legit.ng ta rahoto cewa darakta janar na hukumar NEMA, Mustapha Maihaja ta hanu shugaban sashin labarai na hukumar, Sani Datti ya yi gargadi kan haka sannan yayi kira ga Karin tallafi.

KU KARANTA KUMA: Rundunar 'yan sanda ta cafke mutane 2 da suka yiwa 'yar wata 9 fyade

A halin da ake ciki Legit.ng ta rahoto a baya cewa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a ranar Alhamis, 20 ga watan Satumba ya isa filin jirgin sama na Asaba domin duba wasu yankuna da ambaliyar ruwa yayibarna a jihohin Delta da Anambra.

An tattaro cewa jirgin mataimakin shugaban kasar wanda ya sauka da misalin karfe 1pm don ziyarar aik na kwana gudaya sunduma cikin ambaliyar ruwan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel