Dalilin da yasa ba za mu tsige Saraki ba – Shugaban masu rinjaye a majalisa

Dalilin da yasa ba za mu tsige Saraki ba – Shugaban masu rinjaye a majalisa

- Shugaban masu rinjaye a majalisa, Ahmed Lawan ya ce zaman lafiya ya dawo a majalisa

- Kafin a dawo majalisa Ahmed ya sha alwashin cewa za su tsige Saraki

- Sai dai a yanzu ya ce ya zama dole su binne duk wani rikici don ci gaban kasar

Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Ahmed Lawan a ranar Juma’a, 12 ga watan Oktoba ya bayar da alamun cewa zaman lafiya ya dawo majalisar dokokin kasar sannan kuma cewa babu bakatar tsige shugaban majalisar dattawan, Bukola Saraki.

Kafin dawowa majalisar dokokin kasar a ranar Talata, Lawan ya bayyana a wajen taron jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a daren ranar Asabar cewa APC ba zata bari shugaban majalisar dokokin ya yi mata fin karfin kujerarta ba.

Dalilin da yasa ba za mu tsige Saraki ba – Shugaban masu rinjaye a majalisa

Dalilin da yasa ba za mu tsige Saraki ba – Shugaban masu rinjaye a majalisa
Source: UGC

Yayinda mataimakin shugaban majalisar dattawan, Ike Ekweremadu ya kasance dan jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), shugaban majalisar ma, Bukola Saraki ya sauya sheka daga APC zuwa PDP.

Amma da yake Magana da manema labarai a fadar shugaban kasa a ranar Juma’a, Lawan yace: “Ban san me zan ce maku ba akan rikici amma dai bari na fada maku cewa majalisar dokokin kasar zata ci gaba mayar da hankali kan lamuran kasar, ya zamadole mu zama masu tallafawa kasar, dole mu sanya ra’ayin kasa sama da son rai.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Atiku na ganawar sirri da Peter Obi Yanzu Yanzu: Atiku na ganawar sirri da Peter Obi

Yace ya zama dole su binne duk wani rikici don ci gaban kasar. Ya ce samun banbancin ra’ayi a majalisa ba sabon abu bane domin an hada jam’iyyun siyasa sama da guda a wuri daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel