Rundunar 'yan sanda ta cafke mutane 2 da suka yiwa 'yar wata 9 fyade

Rundunar 'yan sanda ta cafke mutane 2 da suka yiwa 'yar wata 9 fyade

- Kotu ta garkame wasu mutane guda biyu daga garin Tennessee da aka zargesu da yiwa wata yarinya mai watanni 9 fyade

- Mahaifiyar yarinyar ce ta kai rahoton wannan mummunan aika-aikata da mutanen biyu suka yi akan 'yarta ga rundunar yan sanda

- A yanzu dai mutanen biyu na garkame a gidan kaso na Shelby County da ke Amurka

Wasu mutane guda biyu daga garin Tennessee, kasar Amurka, da aka zargesu da yiwa wata yarinya mai watanni 9 fyade, tare da daukar bidiyon yadda suka gudanar da aika aikar, sun fuskanci fushin kotu.

Rahotanni daga FOX13 sun bayyana cewa an gurfanar da Isiah Dequan Hayes, 19 da kuma Daireus Jumare Ice mai shekaru 22, a gaban kotu, bisa aikata laifukan yiwa karamar yarinya fyade da kuma wani laifin fyade makamancin na farko.

Mahaifiyar yarinyar ce ta kai rahoton wannan mummunan aika-aikata da mutanen biyu suka yi akan 'yarta ga rundunar yan sanda a watan Oktoba, 2016, bayan da mahaifiyar ta kalli wani bidiyo da ke nuna yadda Hayes ya ke aikata fasadin ga karamar yarinyar.

KARANTA WANNAN: ICPC ta bankado kimanin N9.8bn da gwamnatin tarayya ta boye a wani banki

Rundunar 'yan sanda ta cafke mutane 2 da suka yiwa 'yar wata 9 fyade

Rundunar 'yan sanda ta cafke mutane 2 da suka yiwa 'yar wata 9 fyade

Mahukunta sun bayyana cewa mahaifiyar ta yi kokari ta gano Hayes a shafin sada zumunta na Facebook, wanda hakan ya sa ta garzawa zuwa ga hukumar 'yan sanda.

Mai shigar da karar, ya ce Ice ne ya dauki bidiyon aika aikar, daga baya kuma rundunar 'yan sanda ta samu nasarar gano Hayes tare da cafke shi a watan Fabureru, wanda kuma ya tabbatar da cewa ya aikata laifin da ake zarginsa da shi.

A yanzu dai mutanen biyu na garkame a gidan kaso na Shelby County da ke Amurka.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel