Abiola watsi yayi da mijina Kingibe, bayan da suka ci zaben 1993 - Ireti Kingibe

Abiola watsi yayi da mijina Kingibe, bayan da suka ci zaben 1993 - Ireti Kingibe

- Mijina bai ci amanar Abiola ba inji Hajiya Ireti Kingibe

- Abiola ne ma yaci amanar mijina, zaku iya tambayar tsohuwar matar shi

- Koda yaci amanar Abiola ma in dai aka yi maganar 12 ga watan yuni, dole ne a hado dashi

Abiola watsi yayi da mijina Kingibe, bayan da suka ci zaben 1993 - Ireti Kingibe

Abiola watsi yayi da mijina Kingibe, bayan da suka ci zaben 1993 - Ireti Kingibe
Source: UGC

Hajiya Ireti Kingibe, tsohuwar matar sakataren Gwamnatin tarayya na wani lokaci ta karyata jita jitar cewa mijinta ya bar MKO Abiola a tsaka da kokarin su na ganin an tabbatar da sakamakon zaben 12 ga watan yuni.

Bayan da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya girmama MKO Abiola da GCFR tare da Kingibe, ana ta kalubalantar cewa Kingibe bai cancanci girmamawar ba saboda barin Abiola da yayi lokacin da suke zirga zirgar tabbatar da sakamakon zaben.

Ireti tace Abiola ne ma ya bar mijinta. A tattaunawar da akayi da ita ta farko bayan shekaru 25 da IBB ya soke zaben, Ireti Kingibe na cewa :"Koda Kingibe ya cancanci girmamawa ko a'a, in har dai za a bada wata girmamawa ga 12 ga watan yuni, toh yana daga ciki. Amma cewa yaci amanar Abiola bai dace ba."

DUBA WANNAN: Jaafar Jaafar ya shiga buya bayan ya fara tsoron ko za'a kashe shi kan bidiyon Ganduje

"Qila da yawan mutane basu ga abinda ya faru dashi ba, kuma bai damu da ya sanar ba. Kowa na cewa Kingibe yaci amanar Abiola, ta yaya? Babu wanda zai iya bayani."

"Idan kuma Kuna so ku sani, akwai tsohuwar matar Abiola, zaku iya tuntubar ta. Shawara ce duk suka yanke, ba wai Kingibe kadai ba, har da su Jakande da kuma wasu daga kungiyar yakin neman zaben Abiola /Kingibe."

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel