Yanzu Yanzu: Atiku na ganawar sirri da Peter Obi

Yanzu Yanzu: Atiku na ganawar sirri da Peter Obi

Dan takarar kujeran shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar na cikin ganawar sirri da Peter Obi a Abuja, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Mista Obi ya isa gidan Atiku dake makwabtaka da Asokoro da misalin karfe 3:00pm sannan su biyun suka shiga tattaunawar da ba’a san na menene ba.

Ana ta rade radin cewa Atiku na son zabar tsohon gwamnan na Anambra a matsayin abokin tafiyarsa.

Labari dake iso mana yanzu shine, Silverbird TV ta rahoto cewa Atiku ya zabi Peter Obi a matsayin abokin takararsa a zabe mai zuwa.

KU KARANTA KUMA: Da dumisa: Kuma dai! Shugaba Buhari ya shiga ganawar sirri da gwamnonin Kano, Ogun da Zamfara

Haka zalika babban jaridar kasuwanci na Najeriya ta ruwaito hakan.

A ranar Lahadi da ya gabata ne tsohon mataimakin shugaban kasar ya zamo dan takarar shugaban kasa a babban jam’iyyar adawa wato PDP

Jama’a na ta tofa albarkacin bakunansu kan wanda ya kamata dan takarar ya zaba a matsayin abokin tafiyarsa daga yankin Igbo ko na Yarbawa.

Zabar Obi da Atiku yayi na zuwa ne sa’o’i 24 bayan ya ziyarci tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, inda ya mara masa baya a matsayin shugaban kasar Najeriya na gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel