2019: Muna bayan Shugaba Buhari - 'Kungiyar Karnukan Motocin haya ta Najeriya

2019: Muna bayan Shugaba Buhari - 'Kungiyar Karnukan Motocin haya ta Najeriya

Da sanadin shafin jaridar Daily Trust mun samu rahoton cewa, kungiyar Karnukan Motocin haya ta Najeriya, BCAN, ta daura damara ta goyon bayan kudirin shugaban kasa Muhammadu Buhari na sake neman kujerar sa a yayin zabe na 2019.

Kungiyar ta Bus Conductors Association of Nigeria, ta bayyana cewa ta kagara ta ga shugaba Buhari ya sake haye kujerar sa ta fadar Villa dake Aso rock garin Abuja.

Shugaba mai kula da harkokin kungiyar na kasa, Mista Israel Adeshola, shine ya bayyana hakan tare da yabawa shugaba Buhari yayin da aka kungiyar yakin neman zaben sa ta kaddamar da shugabannin kungiyar BCAN reshen jihar Delta.

Mista Adeshola yake cewa, ko shakka babu kungiyar yakin neman zaben shugaban kasar ta kudiri aniyyar inganta jin dadin al'ummar kasar nan tare da ba su kariya a sanadiyar kyakkyawan jagoranci na shugaba Buhari.

2019: Muna bayan Shugaba Buhari - 'Kungiyar masu Motocin haya ta Najeriya

2019: Muna bayan Shugaba Buhari - 'Kungiyar masu Motocin haya ta Najeriya
Source: Depositphotos

Yake cewa, kungiyar ta su tana da tabbaci da kyautata zato akan kasar nan wajen samun kyakkyawar makoma da kuma kaiwa zuwa ga tudun tsira a karkashin jagorancin shugaba Buhari.

KARANTA KUMA: 2019: Dankwambo ya taya Atiku murna, ya sha alwashin goyon bayan sa 100 bisa 100

Ya ci gaba da cewa, ba bu wani tafarki da Najeriya za ta cimma wannan mamora face hada kanta wuri guda domin ganin shugaba Buhari ya sake samun nasara ta lashe kujerar sa a yayin zabe na 2019.

A sanadiyar haka Mista Adeshola yake kira ga al'ummar kasar akan su hada kai wuri guda wajen marawa shugaba Buhari baya domin tabbatar da nasarar sa a yayin babban zabe.

Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel