Karin albashi: NLC da TUC sunyi barazanar fara sabuwar yajin aiki

Karin albashi: NLC da TUC sunyi barazanar fara sabuwar yajin aiki

- Kungiyar Kwadago na kasa tayi barazanar sake fara sabuwar yajin aiki cikin 'yan kwanakin nan

- Wannan na zuwa ne bayan kungiyar ta kwadago ta ce gwamnati na kokarin saba alkawarin da tayi a baya

Kungiyar Kwadago na kasa (NLC) da Kungiyar Masu Sana'o'i (TUC) sunyi barazanar sake fara wata sabuwar yajin aiki saboda batun karin albashin na ma'aikata mafi karanci a Najeriya.

Shugaban NLC, Ayuba Wabba ne ya bayyana cewar akwai yiwuwar ma'aikatan za su koma yajin aiki cikin kankanin lokaci bayan an gudanar da taro domin tabbatar da cewa ma'aikatan ba za su cutu ba.

Karin albashi: NLC da TUC sunyi barazanar fara sabuwar yakin aiki

Karin albashi: NLC da TUC sunyi barazanar fara sabuwar yakin aiki
Source: Depositphotos

Kazalika, Wabba ya cacaki Ministan Kwadago, Dr. Chris Ngige inda ya ce ministan ya yi gaban kansa ne wajen fadin cewar gwamnati ba za ta iya biyan N30,000 ba kuma kungiyar ba za ta amince da wani canji kan hakan ba.

DUBA WANNAN: Abinda Obasanjo ya fada min cikin sirri kafin ya goyi baya na - Atiku

A hirar da ya yi da manema labarai jiya a Lokoja wajen kaddamar da gidaje 1,200 na ma'aikatan Bankin bayar da bashin gina gidaje (FMBN), Wabba ya ce abinda Ngige ya fadi ya sha ban-ban da yarjejeniyar da kwamitin albashin ta tsayar.

A ranar Laraba, Ministan ya ce har yanzu ba'a tsayar da adadin albashin mafi karanci da za'a iya biya ba saboda har yanzu ana tattaunawa a maimakon abinda kungiyar kwadago ta fadi na cewar gwamnati ta amince za ta biya N30,000.

Sai dai shi a bangarensa, Wabba ya ce an cimma matsaya kan albashin da za'a biya kuma duk wanda ya ce ba'a cimma matsaya ba, ba gaskiya ya ke fada ba.

A bangarensa, Shugaban TUC, Boboi Bala Kai Gama, ya ce ya yi matukar mamakin yadda gwamnatin tarayya za ta canja alkawarin da tayi kan albashi mafi karancin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel