ICPC ta bankado kimanin N9.8bn na gwamnatin tarayya da aka boye a wani banki

ICPC ta bankado kimanin N9.8bn na gwamnatin tarayya da aka boye a wani banki

- Hukumar ICPC ta ce ta gano N9.8bn mallakin gwamnatin tarayya da aka boye a wani bankin kasuwa

- A cikin shekara ta 2005, gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti don sayar da wasu kadarori mallakin gwamnatin, wasu a ciki da wajen Abuja

- Hukumar ta ce za ta hukunta duk wanda ke da hannu a boye kudaden da zaran ta kammala bincike

Hukumar da aka kafa mai zaman kanta don yaki da cin hanci da rashawa da dangoginta ICPC ta ce ta gano wasu makudan kudade da suka kai N9.8bn, mallakin gwamnatin tarayya da aka boyesu a wani banki mai suna Aso Savings and Loans Plc.

ICPC a cikin wata sanarwa daga mai magana da yawunta, Mrs. Rasheedat Okoduwa, ta bayyana cewa kudaden wadanda aka samesu daga sayar da wasu kadarori na gwamnati, an ajiyesu a bankin kasuwa na Aso Savings and Loans Plc mai makon asususn gwamnatin tarayya.

Hukumar ta ce ta gayyaci babban daraktan bankin, Mr Kunle Adedigba, don tuhumarsa akan wadannan kudade da aka ajiye a bankin nasu.

KARANTA WANNAN: Saboda cutar kwastoma: An rufe gidajen man fetur 30 a garin Benin

ICPC ta bankado kimanin N9.8bn da gwamnatin tarayya ta boye a wani banki

ICPC ta bankado kimanin N9.8bn da gwamnatin tarayya ta boye a wani banki
Source: Depositphotos

Hukumar mai yaki da cin hanci da rasha ta ce bankin ya yi ikirarin cewa bashi da isassun kudaden jarin da zai ci gaba da gudanar da ayyukansa, kuma a shirye yake ya mikawa gwamnatin tarayyar wasu daga cikin kadarorin da ya mallaka.

Sanarwar ta ce, "A cikin shekara ta 2005, gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti don sayar da wasu kadarori mallakin gwamnatin, wasu a ciki da wajen babban birnin tarayya Abuja.

"ICPC ta samu wani korafi akan wannan aiki da aka baiwa kwamitin, wanda a kan hakan ne ta gano cewa kwamitin ya sanya akalla N9.8bn a 2010 da 2014 na kudin kadarorin da aka sayar a bankin Aso Savings and Loans Plc, mai makon ya sanya a asusun gwamnatin tarayya."

Hukumar ta ce za ta hukunta duk wanda ke da hannu a boye kudaden da zaran ta kammala bincike.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel