Saboda cutar kwastoma: An rufe gidajen man fetur 30 a garin Benin

Saboda cutar kwastoma: An rufe gidajen man fetur 30 a garin Benin

- Ma'aikatar masana'antu ta rufe gidajen mai 30 a Benin biyo bayan kamasu da matse litar man da suke sayarwa jama'a

- Jami'in ma'aikatar ya ce sun gudanar da bincike akan akalla gidajen sayar da mai 120

- Nwachukwu ya ce gidajen man da aka rufe, za a sake bude su da zaran ma'aikatar ta kammala gudanar da bincike akan su

Sashen da ke kula da awon nauyi da kiyasci yawan kaya na ma'aikatar masana'antu, kasuwanci da kuma saka hannun jari na kasa, ya rufe gidajen da ake sayar da man fetur 30 a fadin Benin.

Nwachukwu Cordelia, babban jami'in watsa labarai na ma'aikatar masana'antu, kasuwanci da kuma saka hannun jari na kasa, ya bayyana hakan a zantawarsa da kamfanin dilancin labarai na kasa (NAN) a ranar Juma'a a garin Benin.

Nwachukwu, wanda ya isa jihar Edo don sanya ido da kuma yin rangadi a babban birnin jihar, wato Benin, da kuma Auchi da Uromi, ya ce an rufe gidajen man ne sakamakon kamasu da matse litar mai wajen sayarwa kwastomominsu.

Saboda cutar kwastoma: An rufe gidajen man fetur 30 a garin Benin

Saboda cutar kwastoma: An rufe gidajen man fetur 30 a garin Benin

KARANTA WANNAN: Hafsan rundunar sojin kasa Tukur Buratai ya samu lambar yabo ta kwarewar jagoranci

"Mun gudanar da bincike akan akalla gidajen sayar da mai 120, wasu daga cikinsu na yin adalci, yayin da wasunsu ke cutar da masu sayen mai a wajensu. Wannan ne ya sanya muka rufe gidajen man da ke cutar kwastomomi tare da gayyatarsu zuwa ofishinmu don amsa tuhuma.

"Da yawa daga cikin masu gidajen man na dora laifin kacokan akan direbobin tankar mai, bin iska da man yake yi da kuma yawan mutanen da suka hura masu wuta akan bukatu daban daban," a cewar sa.

Nwachukwu ya bayyana cewa gidajen man da aka rufe, za a sake bude su da zaran ma'aikatar ta kammala gudanar da bincike akan su, na sanin dalilin da ya sanya suke matse litar man su don cutar da kwastomominsu.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel