Kishin-kishin: Daya daga cikin gwamonin APC ya fice daga jam'iyyar

Kishin-kishin: Daya daga cikin gwamonin APC ya fice daga jam'iyyar

Wani labari da ba'a tabbatar da sahihancinsa ba da Legit.ng ta samu na cewa gwamnan jihar Ogun, Sanata Ibikunle Amosun ya fice daga jam'iyyar All Peoples Congress (APC) ya koma jam'iyyar Accord Party.

An samo labarin ne daga shafin Twitter (@ogun_state) inda shafin ya ce gidan talabijin na jihar Ogun ne ta ruwaito labarin.

DUBA WANNAN: Tashin hankali: Kotu za ta janye belin da ta bawa tsohon gwamnan PDP

A baya, Legit.ng ta ruwaito cewar gwamna Ibikunle Amosun ya yi barazanar ficewa daga jam'iyyar ta APC muddin kwamitin gudanarwa na jam'iyyar ba ta amince da zabin magajinsa Abdul-Kabir Adekunle Akinlade ba.

An ruwaito cewar gwamnan ya yi barazanar ficewar ne a yayin wata taro da akayi a gidansa da ke Ibara GRA, Abeokuta tare da shugabanin jam'iyyar da wasu magoya bayansa daga kananan hukumomi 20 da ke jihar.

A taron gwamnan ya bayyana wa magoya bayansa sakamakon ganawarsa da shugaba Muhammadu Buhari da shugabanin jam'iyyar APC na kasa amma bai bayyana musu jam'iyyar da zai koma ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel