2019: Dankwambo ya taya Atiku murna, ya sha alwashin goyon bayan sa 100 bisa 100

2019: Dankwambo ya taya Atiku murna, ya sha alwashin goyon bayan sa 100 bisa 100

Biyo bayan nasarar Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa da ya lashe tikitin takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, daya daga cikin manema takarar Gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, ya taya sa murna tare da shan alwashin goyon bayansa 100 bisa 100.

Dankwabo wanda yana daya daga cikin wadanda suka nemi tikitin takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, ya kawar da adawa gefe inda ya taya Atiku murna tare da daura damara da kudirin goyon bayansa a yayin babban zabe na 2019.

2019: Dankwambo ya taya Atiku murna, ya sha alwashin goyon bayan sa 100 bisa 100

2019: Dankwambo ya taya Atiku murna, ya sha alwashin goyon bayan sa 100 bisa 100

Kamar yadda shafin jaridar Vanguard ta ruwaito, Dankwambo ya bayyana kudirin goyon bayan dan takarar jam'iyyar sa ta PDP a zaben 2019 yayin ganawa da manema labarai cikin babban birnin kasar nan tarayya a yau Juma'a.

A cewarsa, Dankwambo wanda ya lashe tikitin jam'iyyar PDP na takarar kujerar Sanatan Gombe ta Arewa, ya bayyana fatansa da kuma kyautata zato da cewar cikin yarda ta Ubangiji jam'iyyar PDP sai tayi nasarar lashe kujerar shugaban kasa a yayin zaben 2019.

KARANTA KUMA: PDP ba ta da halin wanke zunuban Atiku - APC

Tsohon akawun asusun gwamnatin tarayya, na daya daga cikin mutane 13 da suka nemi takarar tikitin kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP da a halin yanzu yake kuma yabawa Atiku dangane da juriya da kuma jajircewarsa akan wannan kudiri da ya sanya a gaba.

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, jam'iyyar APC ta jan gora ta adawa da cewa jam'iyyar PDP ba za ta iya tsarkake duk wasu kurakurai da kuma zunuban da Atiku ya aikata a baya.

Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel