Abinda Obasanjo ya fada min cikin sirri kafin ya goyi baya na - Atiku

Abinda Obasanjo ya fada min cikin sirri kafin ya goyi baya na - Atiku

- Atiku Abubakar ya bayyana abinda ya faru tsakaninsa da Olusegun Obasanjo kafin ya goyi bayansa

- Atiku ya ce Obasanjo a kebe da shi a wani daki inda ya nuna masa jawabin da ya rubuta kuma ya ce ya karanta ya fada masa abubuwan dai bai gamsu da su ba domin ya cire

- Atiku ya ce ya karanta dukkan jawabin kuma ya fadawa tsohon mai gidansa cewar ya gamsu da dukkan abinda ya rubuta a kansa

Dan takarar jam'iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana abinda tsohon mai gidansa, Olusegun Obasanjo ya fada masa cikin sirri kafin ya goyi bayansa kan takarar shugabancin kasa a zaben 2019.

Abinda Obasanjo ya fada min cikin sirri kafin ya goyi baya na - Atiku

Abinda Obasanjo ya fada min cikin sirri kafin ya goyi baya na - Atiku

A jawabin da ya yi yayin taron sa da kwamitin amintattu na jam'iyyar a daren jiya Alhamis, ya ce kafin Obasanjo ya fito fili ya goyi bayansa, ya kebe da shi a wani daki inda ya bukaci ya duba jawabin da zai yi a kansa.

DUBA WANNAN: 2019: Ribadu ya janyewa Dankwambo takara

Atiku ya bayyana cewar tsohon mai gidansa ya ce ya karanta jawabinsa kuma idan akwai abinda bai masa dadi ba zai cire shi daga cikin jawabin kafin ya fito fili ya karanta wa duniya.

Sai dai bayan ya karanta jawabin, Atiku ya bayyana gamsuwarsa da dukkan abinda Obasanjo ya rubuta cikin jawabin.

Atiku ya yabawa tsohon shugaban kasa Obasanjo saboda yadda ya jajirce kan akidarsa da cigaba da riko da halayensa.

Atiku ya shaidawa mambobin kwamitin amintattun cewar zai yi aiki tare da dukkan wadanda su kayi takara da shi a zaben fidda gwani domin dukkansu manufansu abu guda ne wato cigaban Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel