PDP ba ta da halin wanke zunuban Atiku - APC

PDP ba ta da halin wanke zunuban Atiku - APC

A yayin da siyasar kasar nan ta dauki wani sabon salo, jam'iyyar APC ta sake jan gora kan jam'iyyar adawa ta PDP da cewar ba za ta iya tsarkake zunubai da kuma kurakuren da tsohon Mataimakin shugaban kasa ya tafka, Alhaji Atiku Abubakar.

Ko shakka ba bu ana ci gaba da tafka adawa tsakanin manyan jam'iyyun kasar nan biyu yayin da tsohon mataimakin shugaban Najeriya ya lashe tikitin takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP yayin zaben fidda gwani da aka gudanar karshen makon da ya gabata.

A sanadiyar haka cikin wata sanarwa a ranar Alhamis din da ta gabata kakakin jam'iyyar APC na kasa, Yekini Nabena, ya bayyana cewa za a ci gaba da takfa muhawara kan amincin wanda zai jagoranci kasar nan yayin da babban zabe na 2019 ke ci gaba da karatowa.

PDP ba ta da halin wanke zunuban Atiku - APC

PDP ba ta da halin wanke zunuban Atiku - APC
Source: Depositphotos

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, Nabena ya mayar da martani kan wata sanarwa ta kakakin jam'iyyar PDP, Mista Kola Ologbondiyan, da ya kalubalanci kusoshin gwamnatin jam'iyyar APC dake tantamar rashin amincin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP.

KARANTA KUMA: Hukumar Kastam ta datse wasu Motoci na alfarma da Kayan fasakauri a jihar Legas

Nabena ya bayyana cewa, ko kadan jam'iyyar PDP ba za ta iya tsarkake Atiku daga kurakuransa da kuma zunuban da ya aikata musamman na rashawa da kuma yiwa dokokin kasar nan karan tsaye a tsakanin shekarar 1999 zuwa 2006 na gwamnatin su.

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Atiku ya samu sahalewa da amincin tsohon shugaban kasa kuma Ubangidansa, Cif Olusegun Obasanjo, kan kudirin sa na takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP bayan da suka bude sabon shafi na kulla dankon zumunta a tsakanin su.

Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel