Sanata Marafa ya kwancewa Adams Oshiomole da jam’iyyar APC zani a Kasuwa

Sanata Marafa ya kwancewa Adams Oshiomole da jam’iyyar APC zani a Kasuwa

Sanata mai wakiltan mazabar Zamfara ta tsakiya, Kabiru Marafa, ya ce babu ittifkin da akayi a zaben fidda gwanin kujeran gwamnan jihar karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC)

Hukumar INEC ta aikawa jam’iyyar APC wasika cewa ta haramta mata fitar da dan takara a zaben gwamnan jihar Zamfara 2019 saboda rashin gudanar da zaben fidda gwani a jihar cikin lokacin da hukumar ta kayyade.

Marafa yayinda yake magana kan wasikar da shugaban APC, Adams Oshiomole, ya aikawa hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC cewa jam’iyyar tayi ittifaki kan dan takaran gwamnan jihar kafin ranan 7 ga watan Oktoban da hukumar ta kayyade, ya ce karya Oshiomole yake.

KU KARANTA: Ana rade-radin Jam’iyyar PDP ta dakatar da Takai a Jihar Kano

Marafa wanda shima dan takaran kujeran gwamnan ja kwance zanin jam’iyyar a kasuwa inda yace kwamitin da suka wakilci shugaban jam’iyyar a Zamfara basu fada mas gaskiyan abinda ya faru ba.

Yace: “Yan takara tara (9) ne ke neman kujeran. Mutane hudu sun janye, amma babu ittifakin da akayi tsakanin mu biyar da muka rage har akalla rufe zaben.”

“ “Kwamitin sun yi iyakan kokarinsu wajen ittifaki kan mutum daya amma bangarorin biyun basu amince ba.”

“Abinda nike zayyanawa a nan shine idan kukayi kokarin daurawa mutane wani dan takara, za muyi tawaye.”

Yace idan APC na da hujjan zaban dan takara, ga fili ga doki. Amma idan ba za’a nemi mafita ba, sai dai jam’iyyar ta hakura bayan shekaru hudu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel