Zan ci gaba da shugabancin Obasanjo ne idan nayi nasara - Atiku

Zan ci gaba da shugabancin Obasanjo ne idan nayi nasara - Atiku

A lokacin ziyarar da tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar kujeran shugaban kasa na jam’iyyar Peaoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar, ya kai ga tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a ranar Alhamis, 11 ga watan Oktoba ya bayyana cewa zai ci gaba da tsarin mulkin tsohon uwagidan nasa ne idan har yayi nasarar lashe zaben 2019.

Atiku ya kasance mataimakin shugaban kasa a gwamnatin Obasanjo daga 1999 zuwa 2007.

Atiku wanda ya bayyana ziyarar a matsayin mai dunbin tarihi a gare shi, Obasanjo dama kasar, yace ba don horarwa ta tsohon ubangidan nasa bad a kuma damar da ya basa na zama mataimakin shugaban kasa ba toh da bai kai inda yake ba a yanzu.

Zan ci gaba da shugabancin Obasanjo ne idan nayi nasara - Atiku

Zan ci gaba da shugabancin Obasanjo ne idan nayi nasara - Atiku
Source: Facebook

Yace lokaci yayi da ya kamata suyi aiki tare domin sake lamuran kasar zuwa tafarki na gaskiya, hadin kai da kuma ci gaba.

KU KARANTA KUMA: Mazauna Dapchi na murnar ganin gwamnatin tarayya na iya bakin kokarinta don ganin an saki Leah Sharibu

Da yake bayyana ranar a matsayin mafi farin ciki a rayuwarsa, Atiku yayi alkawarin cewa zai ci gaba daga inda shugabancin Obasanjo ya tsaya a 2007.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel