An kama boka bayan da ya kashe wata da yake zargin wai mayya ce

An kama boka bayan da ya kashe wata da yake zargin wai mayya ce

- 'Yansanda sun cafke wani mai wa'azi a jihar Ogun

- Ana zargin Lekan da kashe wata matashiya 'yar shekara 25

- Iyayen yarinyar sun kaita wajen Lekan ne don nema mata magani

An kama boka bayan da ya kashe wata da yake zargin wai mayya ce

An kama boka bayan da ya kashe wata da yake zargin wai mayya ce
Source: Depositphotos

Hukumar yan sanda ta jihar Ogun ta cafke wani mai wa'azi mai suna Lekan Olukolu bisa zargin sa da hallaka Idowu Ogunkoya 'yar shekara 25.

An kama wanda ake zargin ne a ranar Lahadi 19 ga watan Agusta.

'Yansandan sun cafke shi ne biyo bayan karar da iyayen yarinyar suka shigar.

DUBA WANNAN: Jaafar Jaafar ya shiga buya, kan 'bidiyon Ganduje'

Iyayen yarinyar sun kaita wajen Lekan na akan ya bata magani saboda suna zarginta da maita.

Lekan ya bawa yarinyar wani magani inda tanasha ta fadi ta mutu.

Kwamishinan yansandan jihar Ahmed Iliyasu ya bada umarnin a mika karar zuwa sashen bincike dake Abeokuta.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel