2019: Kyau Atiku ya dauko Ike Ekweremadu a matsayin ‘Dan takaran PDP – Inji wani Masani

2019: Kyau Atiku ya dauko Ike Ekweremadu a matsayin ‘Dan takaran PDP – Inji wani Masani

Dazu mu ka samu labari cewa wani Masanin harkar yau da kullum a Najeriya mai suna Majeed Dahiru ya nemi Alhaji Atiku Abubakar ya zabi Ike Ekweremadu a matsayin Mataimakin sa a zaben 2019.

2019: Kyau Atiku ya dauko Ike Ekweremadu a matsayin ‘Dan takaran PDP – Inji wani Masani

Wani ya bada shawara Sanata Ekweremadu ya zama Mataimakin Atiku
Source: Facebook

Dahiru yayi wannan jawani ne a gidan rediyon Ray Power da ke babban Birnin Tarayya Abuja yana mai kira ga ‘Dan takaran Shugaban kasar na Jam’iyyar PDP ya dauko Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa a matsayin Abokin tafiyar sa.

Wannan Masani ya bayyana cewa akwai hikima kwarai da gaske idan har tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku ya dauko Ekweremadu a Jam’iyyar PDP domin kuwa da shi ake yi wa kundin tsarin mulkin kasar nan garambawul.

KU KARANTA: Mai abin fada ba ya fada: Atiku ya fadawa Buhari ayi baja-kolin hujjoji

Malam Dahiru yake cewa Ekweremadu yana da ilmi game da batun da Atiku yake kira a kai na yi wa Najeriya sabon shimfida. Sanata Ekweremadu dai a matsayin sa na rikakken ‘Dan Majalisa zai iya taimakawa Atiku wajen cin ma burin sa.

Da wannan kwararre yake magana a gidan rediyo dazu, ya nuna cewa Ekweremadu ya san siyasa domin kuwa yayi Kansila, ya kuma rike Shugaban Ma’aikatan gidan Gwamnati, ya kuma rike Sakataren Gwamnati har ta kai ya zama Sanata.

Ana dai tunani Sanata Ike Ekweremadu yana da Jama’a musamman a Kasar Inyamurai wanda Atiku zai nemi kuri’un su, sannan kuma ya san aiki matuka gami da cewa yana da suna mai kyau a Kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel