Mazauna Dapchi na murnar ganin gwamnatin tarayya na iya bakin kokarinta don ganin an saki Leah Sharibu

Mazauna Dapchi na murnar ganin gwamnatin tarayya na iya bakin kokarinta don ganin an saki Leah Sharibu

Mazauna garin Dapchi dake jihar Yobe sun ce sun yi imani da kokarin gwamnati wajen ganin an saki Leah Sharibu, yar makaranta guda da ta rage a hannun yan ta’addan Boko Haram.

Hakan ya biyo bayan manyan tawagar gwamnatin taraya da ake sanya ran za su kai ziyara yankin.

Mazauna yankin da suka yi hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a ranar Juma’a, 12 ga watan Oktoba a Dapcbhi sunce kulawar da gwamnatin tarayya ta nuna kan lamarin ya sake sabonta fatansu ga sakin Leah.

Mazauna Dapchi na murnar ganin gwamnatin tarayya na iya bakin kokarinta don ganin an saki Leah Sharibu

Mazauna Dapchi na murnar ganin gwamnatin tarayya na iya bakin kokarinta don ganin an saki Leah Sharibu
Source: Depositphotos

Alhaji Bashir Manzo, shugaban kungiyar iyayen yaran Dapchi, yace gwamnatin tarayya ta jajirce wajen tabbatar da sakin yarinyar.

KU KARANTA KUMA: 2019: Manyan yan Najeriya 4 da suka yi nasarar sasanta Atiku da Obasanjo

Bukar Modu wani mazaunin Dapchi yace “Shugaba Buhari ya tabbatar mana da cewar shi uban kasar ne.

Yagana Modu, mahaifiyar daya daga cikin yara 100 da aka saki da farko tace gwamnatin tarayya ta hankaltar da mutanen Dapchi cewar suna da muhimmanci.

NAN ta ruwaito cewa tawagar gwamnatin tarayya za su ziyarci Dapchi a ranar Juma’a domin ganawa da iyayen Leah Sharibu wacce ke a hannun yan ta’adda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel