Shehu Sani: Ba mu ba Uba Sani satifiket din lashe zaben fitar da gwani ba – Inji APC

Shehu Sani: Ba mu ba Uba Sani satifiket din lashe zaben fitar da gwani ba – Inji APC

Mun samu labari daga ‘Yan jaridun kasar nan cewa Jam’iyyar APC mai mulki ta karyata batun cewa an ba ‘Yan takarar da su ka lashe zaben fitar da gwani takardars shaidar nasara.

Shehu Sani: Ba mu ba Uba Sani satifiket din lashe zaben fitar da gwani na zaben 2019 ba – Inji APC

Kila Uba Sani ba zai yi takarar Sanata a 2019 ba saboda ya kai Jam'iyya Kotu
Source: UGC

Mukaddashin Sakataren yada labarai na APC na kasa baki daya Yekina Nabena ya musanya cewa an ba wasu da su ka lashe zaben fitar da gwani satifiket. Nabena ya karyata wannan ne lokacin da ya zanta da manema labarai jiya.

A jawabin da Yekina Nabena yayi, za a fahimci cewa rikicin Jam’iyyar game da kujerar Sanatan Kaduna ta tsakiya wanda Shehu Sani yake kai yanzu ya sake daukar wani salo bayan Jam’iyyar tace ba ta ba kowa shaidar nasara ba.

A baya dai ana ta yada cewa Jam’iyyar APC ta mikawa Uba Sani satifiket a matsayin shaidar lashe zaben fitar da gwani. Nabena yace babu gaskiya a lamarin domin Jam’iyyar mai mulki ba ta kowa wani satifiket a kaf Najeriya ba.

KU KARANTA: Ba bu ko jam'iyya daya da ta gabatar mana da 'yan takarar ta - INEC

Da aka yi wa babban Jami’in Jam’iyyar maganar cewa Uba Sani sun shiga da kara zuwa Kotu bayan Jam’iyya ta haramta yin zaben fitar da gwani, sai ya maida amsa da cewa za su duba batun tare da daukar matakin da ya dace.

Kakakin na APC dai yace Mai ba Jam’iyya shawara zai yi wa rikicin na Shehu Sani da Uba Sani wanda ya kai gaban Kotu kallo da idanun basira tare da bada shawarar matakin da ya kamata a dauka domin samun masalaha a 2019.

A tsarin APC dai bai halatta ‘Dan Jam’iyya ya kai kara gaban Kotu ba kamar yadda sashe na 21 na dokar Jam’iyya ta bayyana. Don haka wasu Masana shari’a ke ganin cewa Malam Uba Sani ya fado kuma ba zai zama ‘Dan takaran APC ba.

Jiya kun ji cewa babu wani yunkuri da Majalisa ke yi na kokarin tsige Shugaban ta Yakubu Dogara daga matsayin sa saboda kurum ya sauya sheka daga Jam’iyyar APC mai mulki zuwa PDP mara rinjaye.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel