Hukumar Kastam ta datse wasu Motoci na alfarma da Kayan fasakauri a jihar Legas

Hukumar Kastam ta datse wasu Motoci na alfarma da Kayan fasakauri a jihar Legas

Mun samu cewa hukumar Kastam mai hana fasakauri, ta samu nasarar datse wasu Motoci masu garkuwar harsashin bindiga, a tsakanin ranar 4 ga watan Satumba zuwa 3 ga watan Okotoba na wannan shekara da harajin su ya haura N1bn.

Kamar yadda hukumar ta bayyana yayin ganawa da manema labarai na TVC News, ta kuma samu nasarar datse miyagun kayayyaki na fasakauri da jimillar harajin su ta haura N2bn.

Shugaban hukumar reshen jihar, Kwanturola Muhammad Aliyu, shine ya bayyana hakan yayin gabatar da kayayyakin ga manema labarai da suka hadar har da muggan kwayoyi da kayan maye.

Hukumar Kastam ta datse wasu Motoci na alfarma da Kayan fasakauri a jihar Legas

Hukumar Kastam ta datse wasu Motoci na alfarma da Kayan fasakauri a jihar Legas
Source: Depositphotos

Cikin kayayyakin da hukumar ta datse a reshen ta na jihar Legas sun hadar da; Motoci, buhunan shinkafa, man girki, sutura da kuma magunguna da kuma tabar wiwi tuni an mika su ga hukumomin NAFDAC da NDLEA.

KARANTA KUMA: Ba bu ko jam'iyya daya da ta gabatar mana da 'yan takarar ta - INEC

Legit.ng ta fahimci cewa, hukumar Kastam na ci gaba da jajircewa kan kwazon aiki bisa ga tsayuwar daka ta shugaban ta na kasa, Kanal Hamid Ali, da a halin yanzu ya samu lambar yabo da girmamawa dangane da nasarorin da hukumar ta ke ci gaba da samu.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, ajali ya katse hanzarin shugaban hukumar kula da harkokin jiragen kasa, Injiniya Usman Abubakar, da ya riga mu gidan gaskiya a jiya Alhamis cikin babban birnin kasar nan na tarayya.

Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel