Yanzu-yanzu: Gobara a filin jirgin saman Legas, jirgi ya kama da wuta

Yanzu-yanzu: Gobara a filin jirgin saman Legas, jirgi ya kama da wuta

Wata jirgin kamfanin Overland kirar ATR-72 ya kama da wuta a yau Juma'a, 12 ga watan Oktoba 2018 a babba filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke jihar Legas.

Mun samu rahoton cewa wannan gobara ya fara ne misalin karfe 10:30 na safe yayinda ake gyara a jikin jirgin kawai sai ta kama da wuta.

Idanuwan shaida sun bayyana cewa jirgin ta tashi tamkar bam kuma ya bata wurare daban-daban a filin jirgin. Babu wanda ya ji rauni.

Wani idon shaida ya ce: " Wannan babbn gobara ne, rabin jirgin ya kone. Kana wutan ya shafi wasu jirage da ake gyara a wajen."

Yanzu-yanzu: Gobara a filin jirgin saman Legas, jirgi ya kama da wuta

Yanzu-yanzu: Gobara a filin jirgin saman Legas, jirgi ya kama da wuta
Source: Facebook

Wannan annoba na faruwa ne yayinda yan kungiyar kwadagon babban filin jirgin saman suka dawo aiki bayan sun gudanar da zanga-zanga a jiya inda suka hana jirage tashi.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel