Hafsan rundunar sojin kasa Tukur Buratai ya samu lambar yabo ta kwarewar jagoranci

Hafsan rundunar sojin kasa Tukur Buratai ya samu lambar yabo ta kwarewar jagoranci

- Kungiyar masana tattalin arziki ta Nigeria ta karrama Tukur Buratai da babbar lambar yabo ta "Gwarzo wajen iya shugabancin runduna abun ayi koyi."

- Kungiyar ta misalta Buratai a matsayin dodo mai kakkabe 'yannta'addan Boko Haram

- Ya ce hafsan rundunar sojin kasar ya samu gagarumar nasarar da ba a taba samunta a fadin duniya ba

Kungiyar masana tattalin arziki ta Nigeria da ke Ibadan, ta karrama hafsan rundunar sojin kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai da babbar lambar yabo ta "Gwarzo wajen iya shugabancin runduna abun ayi koyi."

Kungiyar ta karrama hafsan rundunar sojin ne a taronta na shekara shekara karo na 10 da ya gudana a kwalejin fasa da kere kere ta gwamnatin tarayya ta Nekede, da ke cikin garin Owerri.

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Farfesa Osisioma Nwolise, shugaban riko na kungiyar wacce aka samawa manema labarai a Abuja, kungiyar ta misalta Buratai a matsayin "Dodo mai kakkabe 'yannta'addan Boko Haram."

KARANTA WANNAN: Yadda kuka hadu haka zaku fadi tare a 2019 - Martanin Buhari ga Obasanjo da Atiku

Hafsan rundunar sojin kasa Tukur Buratai ya samu lambar yabo ta kwarewar jagoranci

Hafsan rundunar sojin kasa Tukur Buratai ya samu lambar yabo ta kwarewar jagoranci
Source: Depositphotos

Nwosile, ya ce sun karrama Buratai da wannan babbar lambar yabo ne biyo bayan "samun nasarar jagorantar rundunar sojin kasar da hadin guiwar sauran jami'an tsaro wajen yaki da ta'addanci, musamman waje murkushe mayakan Boko Haram.

Ya ce hafsan rundunar sojin kasar ya samu gagarumar nasarar da ba a taba samunta a fadin duniya ba, indai aka zo bangaren dakile ta'addi, "a cikin kankanin lokaci, ya kwato yankunan da Boko Haram suka mamaye kafin ya zama hafsan sojin kasar."

Ya yi nuni da cewa irin wannan salo na shugabantar rundunar sojin kasar da Buratai ya ke da shi da kuma, kungiyar ta kuma jinjinawa Buratai akan namijin kokarinsa na bunkasa rayuwar sojojin kasar, iyalansu da kuma manyan jami'an rundunar.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel