Sai an kashe Tiriliyan daya ta daloli sannan wuta zata daidaita a kasar nan - Osinbajo

Sai an kashe Tiriliyan daya ta daloli sannan wuta zata daidaita a kasar nan - Osinbajo

- Har yanzu an kasa shawo kan matsalar lantarki a Najeriya

- Yawancin kasashen Ghana da makwabta sun wuce wannan matsalar

- Najeriya na bukatar jari mai sumbin yawa

Sai an kashe Tiriliyan daya ta daloli sannan wuta zata daidaita a kasar nan - Osinbajo

Sai an kashe Tiriliyan daya ta daloli sannan wuta zata daidaita a kasar nan - Osinbajo
Source: Depositphotos

Matsalar Lantarki a Najeriya, ta kai intaha, inda in aka toshe can, sai can ya bulle, in aka kamo can, sai can ya zame.

A alkawurran da wannan gwamnati ta dauka, kuma ta kasa cikawa, shine, zasu bada wutar lantarki a kullum awa 24, amma shekaru uku kenan abin ya gagara.

Matsalar Lantarkin Najeriya dai gado aka yi, amma abin yaci tura inda ko kashi 10 bisa dari na wutar da ake bukata ba'a iya samarwa.

DUBA WANNAN: Limamiya mace a Turai

A yanzu Mataimakin shugaba Buhari, Farfesa Yemi Osinbajo, ya yanke cewa sai an kashe akalla tiriliyan daya na daloli ne za'a sami wutar lantarki mai dorewa, wannan kudi dai na nufin Tiriliyan 365 na nairori, bajat din kasar nan kuma, N6-8Tr ne a duk shekara.

Sai dai, yace kudaden, a shekaru 29 ne za'a dauka kain a gamma kashe kudin, kuma yana nufin hannayyen jari daga kasashen Turai ne ake bukata su shigo.

Ya fadi hakan ne a taron da ya halarta a Aso Rock, wanda masu ruwa da tsaki na harkar lantarkin ke halarta daga duniya don ganin an farfado da kasar nan, an taimakawa Najeriyar ta sha kan wannan babbar matsala.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel