Jaafar Jaafar, dan jarida mai kwarmato kan zargin cin hancin gwamnan Kano, ya shiga buya
- Wani mawallafin jarida ya boye kansa biyo bayan labarin wani bidiyo daya yada
- Bidiyon wai yana nuni da gwamnan jihar Kano a lokacin da yake karbar cin hanci
- Jaafar ya bayyana cewa akwai wadanda suke kawowa rayuwarsa farmaki

Asali: Twitter
Mawallafin jaridar nan ta Daily Nigerian Jaafar Jaafar, ya shiga hadari biyo bayan wani labari daya wallafa na cewar an ga bidiyo inda gwamnan Kano a lokacin da yake karbar dala har $5m a matsayin cin hanci daga hannun wasu masu.
A rahoton, Mr. Jaafar yace ya sami ganin faifan bidiyo dake nuni da gwamnan a lokacin da yake karbar kudin a lokuta da dama.
Faifan, wanda ba'a sake shi ba, wai ya nuna yadda gwamnan ya fito kansa babu hula ya karbi kudin ya zuba a aljihun sa.
Bincike ya bayyana cewa jaridar Daily Nigeria itace ta fara wallafa wannan labari.
DUBA WANNAN: An rataye masu ta'addanci a Masar
Da majiyarmu ke tattaunawa da Mr Jaafar, ya tabbatar da cewa akwai wadanda suke kawowa rayuwarsa barazana, don haka ya shiga buya, inda a halin yanzu yana wajen da yake akwai tsaro.
Wannan ya janyo hankalin duniya, ciki kuwa har da hukumar kare aiki da hakkokin 'yan jarida dake Amurka a birnin New York.
An zargi cewa Malam Jaafar din, wai yana yi wa Mista Kwankwaso ne aiki don a kayar da gwamnan a zaben badi.
Har yanzu ba'a ji ta bakin hukumomi kan lamarin ba, ko na zargin cin hancin, ko na zargin ana neman ran malam Jaafar din.
Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng