2019: Manyan yan Najeriya 4 da suka yi nasarar sasanta Atiku da Obasanjo

2019: Manyan yan Najeriya 4 da suka yi nasarar sasanta Atiku da Obasanjo

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar kujeran shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya gana da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a ranar Alhamis, 11 ga watan Oktoba a Abeokuta wanda daga bisani aka sanar da cewar sun shirya sabanin dake tsakaninsu.

Koda dai a baya tsohon shugaban kasar ya sha alwashin cewa ba zai marawa Atiku baya ba a kudirinsa na son zama shugaban kasa, bayan ganawar da suka yi ya bayyana cewa ya yafe ma Atiku sannan ya bayyana shi a matsayin zabin sa a zaben 2019.

Obasanjo wanda ya marawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari baya a 2015, ya dade da juya ma shugaban kasar baya inda ya zarge shi da rashin iya tafiyar da tattalin arzikin kasar.

2019: Manyan yan Najeriya 4 da suka yi nasarar sasanta Atiku da Obasanjo

2019: Manyan yan Najeriya 4 da suka yi nasarar sasanta Atiku da Obasanjo
Source: UGC

A cewar jaridar Premium Times, wasu manyan ýan Najeriya ne suka yi nasarar shirya Atiku da tsohon ubangidan nasa.

KU KARANTA KUMA: Ka biya Omo-Agege hakkinsa ko ka gurfana gaban kotu – Alkali ya gargadi Saraki

Wadanda suka halarci taron a Abeoku sun hada da malaman addinin kirista biyu, Matthew Kukah da David Oyedepo; wani malamin Islama, Ahmad Gumi da kuma Ayo Adebanjo shugaban kungiyar Yarbawa, Afenifere.

Ana ganin wadannan shugabanni ne suka yi nasarar sasanta tsakanin Atiku da Obasanjo.

Koda dai wadannan mutane basu fito fili sun marawa Atiku baya ba da farko, an tattaro cewa dukkaninsu ra’ayinsu ya zo guda wajen adawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnatinsa a bayyane.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa wata kungiyar matasa daga kudu maso yamma mai suna South West Youth Assembly (SWYA), ta bukaci dan takarar kujeran shugaban kasa a jam’iyyar the Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar, da ya tabbatar da cewar ya zabi Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose a matsayin abokin takara.

Kungiyar tace Gwamna Fayose ya kasance mafi tsayawa kan maganarsa, mai karfin gwiwa kuma muryar jam’iyyar adawa da ma Najeriya baki daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel