Ba bu ko jam'iyya daya da ta gabatar mana da 'yan takarar ta - INEC

Ba bu ko jam'iyya daya da ta gabatar mana da 'yan takarar ta - INEC

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ta ruwaito hukumar zabe ta kasa watau INEC, Independent National Electoral Commission, ta bayyana cewa kawowa yanzu ba bu wata jam'iyya da ta gabatar mata da jerin 'yan takarar ta da za su fafata a zaben 2019.

Hukumar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa a ranar Alhamis din da ta gabata da sanadin wani Kwamishinan ta na harkokin watsa labarai, Malam Muhammad Haruna.

Ko shakka ba bu hukumar ta kayyade ranar 7 ga watan Oktoba a matsayin rana ta karshe da jam'iyyun siyasa na kasar nan za su kammala zabukansu na fidda gwanayen takara, inda ta kuma bukaci su gabatar da sunayen wadanda suka lashe zabukan a ranar 9 ga watan Oktoba.

Sai dai a yayin da manema labarai suka ziyarci ofishin hukumar domin ganin yadda za ta kaya, ba bu ko jam'iyya guda da ta gabatar da sunayen 'yan takarar ta bisa ga bin umarnin wannan sharadi da hukumar ta gindaya.

Shugaban INEC: Farfesa Mahmoud Yakubu

Shugaban INEC: Farfesa Mahmoud Yakubu
Source: Depositphotos

Legit.ng ta ruwaito cewa, hukumar ta bai wa dukkanin jam'iyyun kasar nan jinkiri zuwa ranar 18 ga watan Oktoba domin gabatar da sunayen 'yan takarar kujerar shugaban kasa da na majalisar tarayya, inda ta kayyade ma su ranar 2 ga watan Nuwamba domin gabatar da sunayen 'yan takarar kujerun gwamna da kuma na majalisar dokoki na jihohi.

KARANTA KUMA: Cikin shekaru 2 an yiwa wata 'Yar shekara 14 fyade sau biyu a jihar Bayelsa

Wata majiyar rahoto ta hukumar ta shaidawa manema labarai cewa, jam'iyyun sun samu tsaikon gabatar da sunayen 'yan takarkarin su a sakamakon dambarwar siyasa da ta biyo bayan zabukan su na fidda gwanayen takara.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, rigima na neman barkewa a jam'iyyar APC reshen jihar Kwara a dalilin 'Dan takarar gwamnan jihar da zai rike tutar jam'iyyar a zaben 2019.

Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel