Ka biya Omo-Agege hakkinsa ko ka gurfana gaban kotu – Alkali ya gargadi Saraki

Ka biya Omo-Agege hakkinsa ko ka gurfana gaban kotu – Alkali ya gargadi Saraki

Babbar kotun tarayya a ranar Alhamis, 11 ga watan Oktoba ta gargadi shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki akan hakkin sanata mai wakiltan Delta ta tsakiya, Ovie Omo-Agege.

Omo-Agege na neman a tura Saraki gidan yari a matsayin hukunci kan sama ma hukuncin kotu na ranar 10 ga watan Mayu wacce ta umurci a dawo da Omo-Agege daga dakatar dashi da aka yi ba bisa ka’ida ba sannan kuma a biya shi hakkinsa na wannan lokacin da aka dakatar da shi.

An shirya sauraron karar a ranar Alhamis, amma wanda akekaran da lauyoyinsa basu hallara a kotu ba.

Ka biya Omo-Agege hakkinsa ko ka gurfana gaban kotu – Alkali ya gargadi Saraki

Ka biya Omo-Agege hakkinsa ko ka gurfana gaban kotu – Alkali ya gargadi Saraki
Source: Depositphotos

Sai dai kuma duk da rashin hallaransa, Justis Nnamdi Dimgba yace yana fatan kara ba shugaban majalisar dattawan wata dama domin ya gyara kuransa ko kuma ya gurfana a gaban kotu domin ya kare kansa.

KU KARANTA KUMA: Rikicin Jos: Majalisa ta nemi Jami’an tsaro su gudanar da bincike a Najeriya

Justis Dimgba ya bayyana cewa tabbass lokaci yayi don sauraron shari’an yayinda takardun kotu sun nuna cewa an aika takarda ga Saraki domin zaman ranar Alhamis din ta hanyar wallafawa a jarida a ranar 25 ga watan Satumba kamar yadda kotu tayi umurni.

Ya kuma umurci Izinyon da ya aika wasika ga shugaban majalisar dattawa ta sashin doka na majalisar dattawa don sanar dasu cewa an dage zaman zuwa ranar 18 ga watan Oktoba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel