Jama’a sun tofa albarkacin bakin su bayan an ga Atiku da Gumi tare da Obasanjo

Jama’a sun tofa albarkacin bakin su bayan an ga Atiku da Gumi tare da Obasanjo

Mun fahimci cewa dinbin Jama’a sun fito sun tofa albarkacin bakin su a makon nan bayan an ga hotunan tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar tare da tsohon Mai gidan sa Olusegun Obasanjo.

Jama’a sun tofa albarkacin bakin su bayan an ga Atiku da Gumi tare da Obasanjo

Atiku Abubakar da wasu sun kai wa Obasanjo ziyara har gida
Source: Facebook

A Ranar Alhamis ne aka hangi Atiku Abubakar wanda yake neman Shugaban kasa a Jam’iyyar PDP a 2019 tare da wasu manyan Malamai Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi da kuma Bishof Mathew Hassan Kukah wajen Obasanjo.

Tuni dai fadar Shugaban kasa tace babu inda wannan hadin-kai na tsofaffin manyan Kasar zai kai. Femi Adesina wanda ke magana a madadin Shugaban kasa yace da Atiku da Cif Olusegun Obasanjo duk sai sun riga rana faduwa a 2019.

Shi kuma wani mai suna Abil Yaminu yace duk ba don Talaka ake wannan ba, yayin da Idi Udofia kuma yake ganin don dai Obasanjo ya rasa yadda ya iya ne kurum ya bi Atiku. Umoren Idongesit kuwa cewa yayi za su zura idanu su sha kallo.

KU KARANTA:

Wani Hadimin Shugaban Majalisar Dattawa watau Bamikole Omisore yace wannan abu yayi daidai domin hadin-kai ake nema. Shi ma dai wani tsohon Minista a Gwamnatin Obasanjo watau Femi-Fani Kayode yayi madalla da zaman.

Wani kuma yace:

Obasanjo ya marawa Shagari baya a 1978 ya kuma yi nasara, ya kuma yi zabe a 1999 ya ci, ya kuma sake takara a 2003 ya dace. Obasanjo ya kuma dauko ‘Yaradua ya ci zabe a 2007, a 2011 ya goyi bayan Jonathan ya kuma yi nasara, da ya marawa Buhari baya a 2015, APC ta ci zabe. Yanzu da yake goyon bayan Atiku, zai yi nasara a zaben 2019.

- UNCLE AJALA

Wani cewa yayi:

Ko ku na so ko ba ku so, Obasanjo yana cikin wadanda su kayi sanadiyyar zaman ‘Yaradua, Jonathan da Buhari, Shugaban kasa a Najeriya don haka Buhari ya tafi kenan.

- @OluwatomiNash

Ka kuma ta bakin wani:

Yau ga Fasto Kukah ana gaisawa da Sheikh Gumi tare da Obasanjo ga kuma Atiku a tsakiya, karshen rabuwar kai a kasar nan ta zo karshe

inji — LasgidiGossip

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo dai yace zai ba Atiku goyon baya kuma ya yafe masa laifin sa. Atiku wanda ya samu sabani da Obasanjo dai yace bai taba farin ciki kamar wannan rana ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel