Cikin shekaru 2 an yiwa wata 'Yar shekara 14 fyade sau biyu a jihar Bayelsa

Cikin shekaru 2 an yiwa wata 'Yar shekara 14 fyade sau biyu a jihar Bayelsa

Za ku ji cewa wani mutum mai shekaru 45 a duniya, Ifeanyi, ya yanki tikitin zama tare da bai wa diga-digan sa hutu a ofishin 'yan sanda na Ekeki dake birnin Yenagoa na jihar Bayelsa bisa laifin yiwa wata budurwa 'yar shekara 14 fyade.

Wannan budurwa mai sunan Gloria kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, ta fuskanci makamancin wannan ibtila'i yayin da wani mutum na daban ya murkushe ta da har ta samu juna biyu da a halin yanzu ta haife tsawon watanni bakwai da suka gabata.

Tashin hankalin na fyade ya sake aukawa wannan budurwa cikin wani Otel dake yankin Ekeke na birnin Yenagoa a ranar Labara da ta gabata.

Gloria tare da jariryar ta 'yar watanni bakwai da ta samu samakon fyaden da aka yi mata na farko

Gloria tare da jariryar ta 'yar watanni bakwai da ta samu samakon fyaden da aka yi mata na farko
Source: UGC

A yayin zayyana yadda lamarin ya auku, Gloria ta bayyana cewa Ifeanyi ya yaudare ta da zummar taimako na sama mata tallafi daga ma'aikatar harkokin Mata ta jihar.

Take cewa, rashin sani ya sanya ta afka cikin wannan mummunan tarko na Ifeanyi da ya dana domin samun damar biyan bukatarsa inda ba tare da aune ba ya keta mata haddi cikin kankanin lokaci.

KARANTA KUMA: Wani Mutum ya tsaya gaban Alkali tare da Surukarsa kan Gadon Matarsa

Legit.ng ta fahimci cewa, makamancin wannan ibtila'i ya aukawa Gloria yayin a take shekaru 13 kacal a duniya, inda a halin yanzu take kira ga duk hukumomi masu ruwa da tsaki akan su kawo mata dauki.

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya shilla kasar Birtaniya domin halartar wani babban taro a fitacciyar jami'ar nan ta duniya watau jami'ar Oxford inda zai gabatar da jawabai kan zuba hannun jari a Najeriya.

Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel