Magoya bayan Yaman sun yi tir da zaben fitar da gwanin APC a Kwara

Magoya bayan Yaman sun yi tir da zaben fitar da gwanin APC a Kwara

Mun samu labari dazu daga Jaridar nan ta Daily Trust ta kasar nan cewa an yi zanga-zanga a Jihar Kwara a dalilin ‘Dan takarar Gwamna da Jam’iyyar APC za ta tsaida a zabe mai zuwa na 2019.

Magoya bayan Yaman sun yi tir da zaben fitar da gwanin APC a Kwara

Yaman ya aikawa Shugabannin Jam’iyya wasika a kan rikicin Kwara
Source: Depositphotos

Magoya bayan daya daga cikin ‘Yan takarar Gwamna a Kwara a karkashin Jam’iyyar APC Alhaji Shuaibu Yaman Abdullahi sun yi tir da zaben fitar da gwani da aka yi. Magoya bayan ‘Dan takarar sun ce an yi mina-mina a zaben.

Shugaban yakin neman zaben Shuaibu Yaman Abdullahi a Jihar ta Kwara ya aikawa Jam’iyyar APC mai mulki wasika inda ya koka da yadda da aka gudanar da zaben tsaida ‘Dan takara a Jihar wanda yace cike yake da rikici.

KU KARANTA:

A takardar Bode Towoju wanda shi ne Darektan takarar Yaman Abdullahi, ya bayyana cewa mutanen su sun gamu da barazana wajen zaben sannan kuma an yi mugudi na kin-karawa wajen tsaida ‘Dan takarar Jam’iyyar.

Wannan karo dai an tsara cewa Gwamna ya fito daga Arewacin Jihar Kwara. Tuni dai Ministan yada labarai Alhaji Lai Mohammed yace Jam’iyyar APC ce za ta lashe zaben Jihar Kwara a 2019.

Mun ji cewa an fara rikici a Jam’iyyar APC ta Jihar Kwara. Tsohon babban Sakataren yada labaran na Jam’iyyar APC Minista Alhaji Lai Mohammed ya nuna cewa Jam’iyyar APC ce za ta lashe zaben Jihar Kwara a 2019 komai runtsi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel