Tallar Najeriya: Osinbajo zai shilla wata babbar jami’a ta duniya dake kasar Birtaniya

Tallar Najeriya: Osinbajo zai shilla wata babbar jami’a ta duniya dake kasar Birtaniya

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osibanjo ya shilla kasar Birtaniya bias gayyata ta musamman da ya samu daga hukumar babbar jami’ar da tafi shahara a Duniya, watau Oxford University, inda zai gabatar da jawabi na musamman akan zuba hannun jari a Najeriya.

Hakazalika majiyar Legit.ng ta ruwaito mataimakin shugaban na Najeriya zai yi Karin haske game da kokarin da gwanatin Najeriya ke yi da tsare tsare ta wajen cigaban al’umma a kasar.

KU KARANTA: Obasanjo ya bayyana muhimman dalilai 5 da suka sa ya gafarta ma Atiku gabanin zaben 2019

Tallar Najeriya: Osinbajo zai shilla wata babbar jami’a ta duniya dake kasar Birtaniya

Osibanjo
Source: UGC

Bugu da kari a yayin taron, Osibanjo zai kaddamar da kwamitin gudanarwar na cibiyar jami’ar Oxford dake nahiyar Afirka, wanda ta kunshi mambobi daga sassan Afirka daban daban wadanda suka shahara a fannoni daban daban.

Daga cikin mambobin kwamitin akwai shugabanta, Tito Mboweni bakar fata na farko daya fara shugabantar babban bankin kasar Afirka ta kudu, kuma tsohon ministan kwadago a zamanin mulkin Nelson Mandela, sauran yayan kwamitin sun hada da:

Gwamna Nasir El-Rufai

Alex Duncan, daga kasar Birtaniya

Ivor Agyeman-Duah, daga kasar Ghana

Uwargidar shugaban kasar Namibia, Madame Monica Geingos

Gareth Ackerman, shugaban kamfanin Pick’n Pay daga kasar Afirka ta kudu

Dakta Charlotte Harland-Scott, Uwargidar tsohon shugaban kasar Zambia

Farfesa Ibrahim Gambari, tsohon mataimakin sakataren majalisar dinkin duniya

Linda Mabhena-Olagunju, shugaban kamfanin DLO Energy Group (Pty) Ltd, daga kasar Afirka ta kudu

Mataimakin shugaban jami’ar Oxford, Roger Goodman ne zai karbi bakoncin mataimakin shugaban Najeriya a yayin da ya isa kasar Birtaniya a wannan ziyara mai matukar muhimmanci ta tallata aikace aikacen Najeriya.

Daga karshe Osibanjo a jawabinsa zai tabo nasarorin da gwamnatin Najeriya a karkashin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta samu a fannonin cigaban al’umma, da tsare tsare tallafi da suka bullo da shi kamar N-Power daya kunshi biyan matasa dubu dari biyar albashin N30,000 duk wata.

Sauran tallafin da gwamnatin Buhari da Osibanjo ta kirkiro sun hada da tallafin naira dubu biyar biyar ga talakawa gajiyayyu, bashin naira dubu goma goma ga kananan yan kasuwa wanda ba shi da ruwa, ciyar da daliban firamari na makarantun gwamnati miliyan 9 kyauta.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel