Ana rade-radin Jam’iyyar PDP ta dakatar da Takai a Jihar Kano

Ana rade-radin Jam’iyyar PDP ta dakatar da Takai a Jihar Kano

A jiya ne mu ka ji cewa Jam’iyyar PDP ta zabi Salihu Sagir Takai a matsayin wanda zai rike mata tuta a zaben 2019. Sai dai kuma yanzu labari akasin haka ya kai gare mu daga wata Majiyar dabam.

Ana rade-radin Jam’iyyar PDP ta dakatar da Takai a Jihar Kano

Ana rade-radin PDP ta dakatar da Salihu Takai Kano
Source: Depositphotos

Mun ji cewa Jam’iyyar PDP ta tabbatar da cewa har yanzu Abba Kabir Yusuf ne ta sani a matsayin ‘Dan takarar ta na Gwamna a Jihar Kano a zaben 2019. Abba K. Yusuf dai shi ne Surukin tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso.

Wani babban Jami’i na Jam’iyyar PDP mai adawa a Hedikwata ya bayyanawa wata Majiyar mu cewa Jam’iyyar ba ta canza sunan Surukin Kwankwaso da Malam Salihu Takai ba kamar yadda rade-radi ya bi ko ina a tsakiyar makon nan.

KU KARANTA: Kwankwaso ya yi barazanar fita daga PDP idan aka canza 'Dan takara

Labarin da mu ke ji shi ne ma dai ana rade-radin cewa Jam’iyyar PDP ta dakatar da ‘Dan takarar da ake cewa an ba tuta daga baya watau Salihu Sagir Takai tare da tsohon Shugaban Jam’iyya na Jihar Sanata Sanata Mas’ud El-Jibril Doguwa.

Ba mu dai iya tabbatar da gaskiyar wannan dakatarwa da aka ce an yi wa manyan na PDP ba a dalilin yunkurin sake gudanar da zaben fitar da gwani da su kayi bayan an rufe kofar tsaida ‘Dan takara a Kasar yayin da ake ta zanga-zanga a Jihar.

A baya dai an yi zabe wanda Abba Yusuf yayi nasara, sai dai ‘Yan takarar Gwamna a Jihar Kano a karkashin Jam’iyyar ta PDP sun yi watsi da sakamakon zaben wanda aka yi a cikin gidan Surukin tsohon Gwamnan Jihar Kwankwaso.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel