Ba zan halarci bikin rantsar da Fayemi ba saboda kar yan siyasa su wulakanta ni - Fayose

Ba zan halarci bikin rantsar da Fayemi ba saboda kar yan siyasa su wulakanta ni - Fayose

- Gwamna Fayose na jihar Ekiti ya ce ba zai samu damar halartar bukin rantsar da magajin kujerarsa ba

- Ya ce zuwa wajen taron zai baiwa yan siyasa damar ci masa fuska wanda kuwa hakan zai lalata dangantaka ne

- Haka zalika ya ce a ranar da za ayi rantsuwar, a ranar ne zai gurfana gaban hukumar EFCC kan wani zargi da ake masa

Gwamnan jihar Ekiti mai barin gado, Mr Ayodele Fayose ya bayyana matsayarsa cewa ba zai halarci bukin rantsar da magajin kujerarsa ba Dr. Kayode Fayemi, wanda aka shirya gudanarwa a ranar 16 ga watan Oktoba, 2018 a cikin jihar.

Gwamnan ya bayyana wannan matsayar tasa ne a ranar Alhamis, a lokacin da ya zantawa da manema labarai a Ado Ekiti, yana mai cewa ba zai halarci bukin rantsarwar bane don gujewa tayar da zaune tsaye, cin fuska da kuma hantara daga yan siyasa.

Fayose ya kara da cewa duk da irin tarin burukan da ya ke da su akan jihar, zai kasance mutum mai farin ciki bayan ficewarsa daga ofishin gwamnan jihar a ranar 16 ga watan Oktoba, 2018.

KARANTA WANNAN: Kotu ta tursasa gwamnan Kogi mayar da sakatarorin da ya tilastawa ritaya a bakin aiki

Ba zan halarci bikin rantsar da Fayemi ba saboda kar yan siyasa su wulakanta ni - Fayose

Ba zan halarci bikin rantsar da Fayemi ba saboda kar yan siyasa su wulakanta ni - Fayose
Source: Depositphotos

Gwamnanya ce ya sha alwashin mika kansa ga hukumar da ke yaki da masu yiwa dukiyar al'umma zagon kasa EFCC a ranar 16 ga watan Oktoba, wanda kuma ranar taci karo da ranar rantsuwar magajin kujerarsa.

A cewar sa, "Yan siyasa na da ban haushi, idan da ace zan halarci wannan taron, wasu daga cikin yan siyasar na iya amfani da wannan damar don cimun fuska koda kuwa ba Fayemi ne ya turo su ba.

"Yin hakan kuwa zai kara lalata dangantaka ne. Matsalolin da ke tsakanina da Fayemi ba wai na kashin kai bane. Ina matukar biyayya ga kwamitin da Fayemi ya kafa na karbar komai daga wajena don barin kujerar gwamnan jihar.

"Haka zalika, zan mika kaina ga ofishin hukumar EFCC da ke Abuja a ranar Talata. Kuma a shirye nake na fuskanci kowanne kwamiti gwamna mai jiran gado ya kafa don tuhumar mulkin jihar karkashin gwamnati na," a cewar Fayose.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.naija.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel