Bankin duniya ya fadin inda Najeriya ta ke a jerin kashashen da suka fi a fannin cigaban al'umma

Bankin duniya ya fadin inda Najeriya ta ke a jerin kashashen da suka fi a fannin cigaban al'umma

A wani sabon daftari da babban bankin duniya ya fitar na jerin kasashen da suka fi a wajen fannin cigaban al'umma, ya ayyana cewa Najeriya na a matsayi na 152 a cikin kasashe 157 da ke a cikin daftarin.

Wannan dai na nufin cewa kasar ta Najeriya na a matsayi na 5 a wajen tabarbarewar rayuwar al'ummar jihar kenan duk kuwa da irin namijin kokarin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke ikirarin yi a dukkan fannoni.

Bankin duniya ya fadin inda Najeriya ta ke a jerin kashashen da suka fi a fannin cigaban al'umma

Bankin duniya ya fadin inda Najeriya ta ke a jerin kashashen da suka fi a fannin cigaban al'umma
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Aikin ginin sabuwar matatar man fetur ya kankama a Najeriya

Legit.ng ta samu cewa Shugaban babban bankin na duniya Dakta Jim Yong Kim shine ya bayyana hakan a garin Bali, kasar Indonisia a wajen taron da bankin ke shiryawa na masa daga sassa daban daban na duniya a duk shekara.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa shima dai dan takarar shugabacin kasar ta Najeriya a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya soki gwamnatin ta Shugaba Buhari inda kuma ya zarge ta da jefa yan Najeriya cikin matsanancin talauci.

A wani labarin kuma, Shugaban kasar tarayyar Najeriya, Muhammadu Buhari a jiya ya roki malaman addinai a Najeriya da su taimaka ma gwamnatin sa wajen ganin ta yi nasa a yakin da take yi da 'yan ta'addan dake boyewa cikin rigar addini.

Shugaban kasar yayi wannan roko ne a lokacin da ya karbin bakuncin shugabannin kungiyar Qdiriyya ta Afrika a karkashin jagorancin shugaban ta Sheikh Qribullah Nasiru Kabara a fadar sa dake a garin Abuja.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel