Goyyawa Atiku baya: Tsinuwar Obasanjo zata koma kan sa - Babban lauya, Keyamo

Goyyawa Atiku baya: Tsinuwar Obasanjo zata koma kan sa - Babban lauya, Keyamo

- Festus Keyamo, kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaba Buhari da yi watsi ga batun goyawa takarar Atiku baya da tsohon shugaban kasa Obasanjo ya yi

- Keyamo ya bukaci 'yan Najeriya su taya Obasanjo da add'uar samun karbuwar tsinuwar da ya taba fatan ta fada masa idan ya taba goyon bayan takarar Atiku

- Kazalika ya zargi shugabannin addinin da suka raka Atiku wurin Obasanjo da shiga siyasar jam'iyya

Festus Keyamo, kakakin kwamitin kamfen din shugaba Buhari ya bayyana cewar tsinuwar da tsohon shugaban kasa Obasanjo ya taba yiwa kansa idan ya goyi bayan takarar Atiku za ta tabbata a gare shi.

A wani jawabi da Keyamo ya fitar a au, Alhamis, 11 ga watan Oktoba, ya yi watsi da batun goyon bayan takarar tiku da Obasanjo ya yi tare da nuna mamakinsa a kan hakan, ganin yadda a baya tsohon shugaban kasar ke alakanta tsohon mataimakin nasa da cin hanci da rashawa.

Goyyawa Atiku baya: Tsinuwar Obasanjo zata koma kan sa - Babban lauya, Keyamo

Babban lauya, Festus Keyamo
Source: Facebook

Babban lauyan ya kara cewar azarbabin da jam'iyyar PDP ke yi na neman sahalewar Obasanjo y tabbatar wa da 'yan Najeriya cewar burinsu shine mayar da Najeriya gidan jiya, kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.

A cewr Keyamo, a shekarar 2014, shugaba Buhari ya ziyarci wasu fitattun 'yan Najeriya domin nuna girmamawa amma bai taba rokon wani ya yafe masa komai ba kamar yadda yanzu Atiku ya bi Obasanjo har gida domin rokonsa gafara.

DUBA WANNA: Canja dan takarar gwamnan a Kano: Masoya Kwankwaso sun fara kona katinansu na PDP, hotuna

Keyamo ya bukci 'yan Najeriya su taya Ovasanjo neman samun tsinuwar da ya taba yi ta samu karbuwa.

A yau ne Atiku, tare da rakiyar wasu manyan addinan Islama da na Kirista da shugabannin jam'iyyar PDP, su ka ziyarci Obasanjo a gidansa dake Abeokuta, jihar Ogun, domin neman afuwa da kuma goyon bayan takarar Atiku a zaben shekarar 2019.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel