Wata sabuwa: Akwai yiwuwar a soma sayar da litar man fetur Naira 205

Wata sabuwa: Akwai yiwuwar a soma sayar da litar man fetur Naira 205

A yadda ake tafiya yanzu akwai yiwuwar litar man fetur a fara saida ta akan Naira 205 duna da yadda farashin gangar danyen man ta tashi a kasuwannin duniya a 'yan kwanakin nan idan dai har gwamnatin tarayyar Najeriya ta yanke shawarar dena biyan kudin tallafin man fetur din.

Yanzu dai kamar yadda majiyar mu ta Punch ta ruwaito mana, kowace litar man da ake shigowa da shi daga kasashen waje zuwa Najeriya ta kai Naira 205 din wanda kuma hakan ya jaza matsin lamba sosai a bangaren hukumar dake kula da albarkatun man fetun din ta kasa watau NNPC.

Wata sabuwa: Akwai yiwuwar a soma sayar da litar man fetur Naira 205

Wata sabuwa: Akwai yiwuwar a soma sayar da litar man fetur Naira 205
Source: UGC

KU KARANTA: Ambasadan Najeriya akasar Girka ya mutu

Legit.ng ta samu cewa tuni dai daman yan kasuwa a Najeriya suka dena shigo da tataccen man fetur din saboda rashin ribar da ke a cikin harkar yanzu tun bayan da gwamnatin tarayya ta ce ta cire tallafin akan man fetur din a shekarar 2016.

Masana dai na ganin cewa tuni man ya wuce wannan farashin na Naira 145 da gwamnatin ta kayyade amma suka cigaba da biyan kudaden tallafin a asirce, lamarin da ya haifar da cece-kuce a lokutan ba.

A wani labarin kuma, Hadaddiyar kungiyar nan ta 'yan kabilar yarbawa dake da'awar kare hakkin su da mutuncin su a Najeriya mai suna Afenifere ta yi fata-fata da tsohon gwamnan jihar Legas, kuma jigo a jam'iyyar APC, Cif Bola Ahmed Tinubu.

Kungiyar ta Afenifere tana tsokaci ne akan kalaman da jigon na APC yayi game da takaddamar da ake fama da ita a kasar ta tsakanin fulani da manoma akan wuraren kiwo.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel