Tashin hankali: Kotu za ta janye belin da ta bawa tsohon gwamnan PDP

Tashin hankali: Kotu za ta janye belin da ta bawa tsohon gwamnan PDP

Alkalin babban kotun tarayya da ke zamansa a Gusau, Justice Fatima Murtala Aminu tayi barzanar janye belin da ta bawa tsohon gwamnan jihar Zamfara, Mahmud Aliyu Shinkafi saboda rashin bayyana a kotu.

An gurfanar da Shinkafi tare da wasu mutane uku Ambassador Bashir Yuguda, Ibrahim Mallaha da Aminu Ahmed Nahuche inda ake zarginsa da karbar N450,000,000 (N450m) daga hannun tsohuwar Ministan Man Fetur, Diezani Alison-Madueke gabanin zaben 2015.

Bayan an gurfanar da su gaban kotu kuma an karanto musu zargin, dukkansu uku sun musanta aikata laifin hakan yasa kotun ta dage cigaba da sauraron karar ziwa ranar 27 ga watan Yunin 2018.

Tashin hankali: Kotu za ta janye belin da ta bawa tsohon gwamnan PDP

Tashin hankali: Kotu za ta janye belin da ta bawa tsohon gwamnan PDP
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Wasu gwamnoni na neman tsige Oshiomhole - Ministan Buhari

A ranar 27 ga watan Yunin, lauya mai kare Shinkafi, Ahmed Raji SAN ya sake shigar da kara inda ya ke kallubalantar hallarcin kotun na sauraron karar da aka shigar.

Wannan dalilin ya sa aka sake dage sauraron karar zuwa ranar 10 ga watan Oktoba amma a ranar sai daya daga cikin wanda suka tsayawa Shinkafi yayin da za'a bashi beli ya shaidawa kotu cewa tsohon gwamnan ya tafi Abuja saboda hallarta taro kan halin tabarbarewar tsaro a jihar.

Hakan ya sa Alkalin kotun tayi gargadi da kaukausan murya inda ta ce kotun ba za ta amince da hakan a nan gaba ba, inda ta kara da cewar idan hakan ya sake faruwa za ta janye belin da aka bawa Shinkafi.

Daga karshe, Justice Aminu ta sake dage cigaba da sauraron Shari'ar zuwa ranar 21 ga watan Nuwamban 2018.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel