Yanzu-Yanzu: Fadar shugaban kasa ta yi magana game da taron Atiku da Obasanjo

Yanzu-Yanzu: Fadar shugaban kasa ta yi magana game da taron Atiku da Obasanjo

- Fadar shugaban kasa ta yi magana game da taron Atiku da Obasanjo

- Fadar tace yadda suka hadu a haka kuma dukkan su za su sha kunya a 2019

- Sun ce su haryanzu talaka na tare da su

Fadar shugaban kasar tarayyar Najeriya a karkashin shugabancin Muhammadu Buhari da daren yau tayi tsokaci game da taron Atiku da kuma Obasanjo da suka gudanar yau a gonar tsohon shugaban kasar a garin Ota dake Abekutta, jihar Ogun.

Yanzu-Yanzu: Fadar shugaban kasa ta yi magana game da taron Atiku da Obasanjo

Yanzu-Yanzu: Fadar shugaban kasa ta yi magana game da taron Atiku da Obasanjo
Source: Facebook

KU KARANTA: Yarbawa sun fara juyawa Tinubu baya

A cikin wata sanarwa da mai taimakawa shugaban kasar na musamman kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu ya sanyawa hannu, ya kuma bayyana cewa goyon bayan da Obasanjo ya baiwa Atiku ba zai yi wani tasiri ba a zaben na 2019.

Legit.ng ta samu cewa a cikin takardar sanarwar, fadar ta shugaban kasa ta kara da cewa su daman tuni sun yi tunanin hakan zata faru domin dukkan su basu son cigaban kasa da kuma talaka wanda gwamnatin Buhari a halin yanzu ke kokarin taimakawa.

Idan dai mai karatu bai manta ba a dazu ne mataimakin shugaban kasar kuma dan takarar shugabancin kasar Najeriya a jam'iyyar PDP, ALhaji Atiku Abubakar ya gana da tsohon shugaban kasar Najeriya Cif Obasanjo tare da rakiyar manyan malaman addinan kasar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel