Kotu ta tursasa gwamnan Kogi mayar da sakatarorin da ya tilastawa ritaya a bakin aiki

Kotu ta tursasa gwamnan Kogi mayar da sakatarorin da ya tilastawa ritaya a bakin aiki

- Babbar kotun masana'antu da ke Lokoja ta janye hukuncin gwamnatin jihar Kogi na tursasa wasu manyan sakatarorin jihar yin ritaya

- Kotun ta ce sashe na 208 (1) (2) na dokar kundin tsarin mulkin kasar na 1999 ya bayar da yancin tsigewa ne ba wai tursasa ritaya ba

- Haka zalika kotun ta baiwa gwamnan jihar umurnin gaggawa na mayar da sakatarorin bakin aikinsu tare da biyansu hakkokinsu cikin kwanaki 60

Babbar kotun masana'antu ta kasa da ke da zama a Lokoja, jihar Kogi, a ranar Alhamis dinnan ta janye hukuncin da gwamnatin jihar ta yanke akan wasu manyan sakatarorin jihar na tursasasu yin ritayar dole alhali lokacin yin hakan bai yi ba.

Mai shari'a Zainab Bashir ce ta yi watsi da wannan hukunci na tursasa ma'aikatan yin ritayar dole, a hukuncin da ta zartas, kan karar da aka shigar gabanta mai lamba NIC/LKJ/10/2017.

Ta ce gwamnatin jihar ba ta da wani cikakken iko na tursasa manyan sakatarorin guda 4 yin ritaya ba tare da wa'adin aikinsu ya kare ba.

Mrs. Bashir ta ce ritayar da gwamnatin jihar ta bada umurni sakatarorin su yi ta hanun hukumar ma'aikata ta jihar, ya saba dokokin aikin gwamnati.

KARANTA WANNAN: Zaben 2019: Darasi 5 da ganawar Obasanjo da Atiku za ta koyar

Kotu ta tursasa gwamnan Kogi mayar da sakatarorin da ya tilastawa ritaya a bakin aiki

Kotu ta tursasa gwamnan Kogi mayar da sakatarorin da ya tilastawa ritaya a bakin aiki
Source: Twitter

Ta ce sashe na 208 (1) (2) na dokokin kundin tsarin mulkin kasar na 1999 kamar yadda aka sake masa fasali, wanda gwamnan jihar ya dogara da shi na tursasa manyan sakatarorin yin ritaya, ya bayar da umurnin tsige su ne kawai, amma ba a yi masu ritaya kai tsaye ba.

Mai shari'ar ta ce akwai babban banbanci tsakanin tsigewa da ritaya.

Ta ce tsigewa itace sauyawa jami'i wurin aiki daga wani mataki zuwa wani mataki, yayin da ita kuwa ritaya ke nufin kammala aikin gwamnati bayan cika shekaru 60 da haihuwa ko shekaru 35 da zama a cikin aikin gwamnati.

Da wannan ne Mrs. Bashir, ta bada umurnin gaggawa na gwamnatin jihar ta mayar da manyan sakatarorin a bakin aikinsu tare da biyansu hakkokinsu, a cikin kwanaki 60.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.naija.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel