Muhimman abubuwa 12 da Obasanjo ya fadi a jawabinsa yayin ganawarsa da Atiku

Muhimman abubuwa 12 da Obasanjo ya fadi a jawabinsa yayin ganawarsa da Atiku

A yau, Alhamis ne tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya dau alkawarin mara wa Atiku baya a matsayinsa na dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2019 mai zuwa.

Obasanjo ya bayar da wannan sanarwan ne yayin da ya ke yiwa manema labarai jawabi bayan kammala taron sirri tsakaninsa da Atiku da wasu jiga-jigan PDP har ma da wasu mallaman addini da wasu manyan 'yan Najeriya.

Matakin na Obasanjo ya bawa mutane mamaki duba da yadda tsohon shugaban kasar ya yi ta nanatawa cewar idan ya goyi bayan Atiku Allah ba zai yafe masa ba.

Abubuwa 20 da Obasanjo ya fadi a jawabinsa yayin ganawarsa da Atiku

Abubuwa 20 da Obasanjo ya fadi a jawabinsa yayin ganawarsa da Atiku
Source: Facebook

Ga dai wasu muhimman abubuwa 12 da Obasanjo ya fadi a jawabin da ya yi bayan ganawa da Atiku.

1. Ina son in taya Atiku murnar nasarar da ya yi a zaben fidda gwani na PDP kuma na gamsu da jawabinsa da ya yi bayan lashe zaben.

2. Tsarin da muka yi a farko, Atiku ne ya kamata ya maye gurbina kuma a yau mun tattauna kan kurakuren da Atiku ya yi a baya.

3. Na gamsu cewar tsohon mataimakina ya sauya halayensa kuma na gamsu da mutumin da ya zama a yau.

4. Kamar yadda na fadi a baya, ba laifin da Atiku ya yi min bane ya babban matsala, laifin da ya yiwa jam'iyya da gwamnati da al'ummar Najeriya ce ta fi damu na.

5. Na yanke shawarar goyon bayan Atiku ne saboda sabbin halayensa da kuma halin da ya tsinci kansa. Nayi imancin cewar matakin da na dauka itace mafi alheri ga Najeriya.

6. A ganawar da mu kayi a yau, ka nuna nadama, ka roki in yafe maka kuma ka bayyana cewar ka koyi darrusa daga abinda ya faru a baya kuma zaka tabbatar hakan bai sake faruwa ba.

DUBA WANNAN: Wasu gwamnoni na neman tsige Oshiomhole - Ministan Buhari

7. A matsayina na Kirista wanda ke neman gafarar Allah a ko yaushe, nima na yafe maka dukkan laifukan da ka yi min a baya kuma ina fatan za ka kiyaye gaba.

8. Bisa ga dukkan alamu, kayi sulhu da jam'iyyar PDP hakan yasa a yau ka yi nasarar zama dan takarar shugbancin kasa a jam'iyyar.

9. Baya da godiya ga abinda jam'iyya tayi maka, ina baka shawarar ka hada kai da sauran wadanda su fafata da kai a zaben fidda gwani domin kuyi aiki tare.

10. Har yanzu akwai wasu matsaloli da ya kamata ka warware a gida Najeriya da kasashen waje kuma idan akwai inda ka ke bukatar in taimaka maka a wannan fanin, a shirye na ke in yi hakan.

11. A ra'ayina, cikin dukkan 'yan takarar PDP, kai ne kafi su wayewa, kwarewar aiki kuma kana cikin shiri domin tunkarar abinda zai zo a gaba.

12. Ina rokon ka ka kasance mutum mai riko da gaskiya, nagarta da kuma biyaya ga dokan Najeriya kuma ba za ka nuna banbanci tsakanin yankunan Najeriya ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel