Sabon rikici na iya barkewa a fadar shugaban kasa da majalisar dattawa kan kudin zabe

Sabon rikici na iya barkewa a fadar shugaban kasa da majalisar dattawa kan kudin zabe

A ranar Alhamis, 11 ga watan Oktoba ne majalisar dattawa ta amince da naira biliyan 189.2 a matsayin kudin hukumar zabe mai zaman kanta na gudanar da zaben 2019.

Hakan na zuwa ne yayinda sabani ya gibta tsakanin fadar shugaban kasa da majalisar dokokin kasar kan kasafin kudin zaben.

Sai dai majalisar dattawan ba ta amince da kasafin kudin jami'an tsaro da Shugaba Muhammadu Buhari ya mika masu ba a ranar Laraba.

Sabon rikici na iya barkewa a fadar shugaban kasa da majalisar dattawa kan kudin zabe

Sabon rikici na iya barkewa a fadar shugaban kasa da majalisar dattawa kan kudin zabe

Haka kuma, majalisar ta kara naira biliyan 45.5 a kan naira biliyan 189 da kwamitin majalisar kan INEC ta gabatar da farko.

Hakan ya sa gaba daya kudin da majalisar ta amince zuwa naira biliyan 234.5, saboda haka ake ganin za’a iya sake samun ballewar sabon rikici daga bangarorin biyu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta amince da N234.51bn na INEC

Majalisar dai ta amince da kasafin kudin ne bayan da shugaban kwamitin kasafin kudi, Danjuma Goje ya mika rahoton da kwamitinsa ya hada bayan duba wasikar da Shugaba Buhari ya aika wa majalisar.

A na kuma sanya ran cewa zuwa mako mai zuwa ne majalisar za ta amince da kasafin kudin jami'an tsaron.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel