UBE zata raba N150b ga jihohi don ilimi kyauta - Ministan Ilimi

UBE zata raba N150b ga jihohi don ilimi kyauta - Ministan Ilimi

- UBEC zata raba Naira biliyan 142.58 domin tallafawa cigaban ilimi a jihohin fadin kasar nan

- Bankin duniya ma ta bada dala miliyan 611 bashi domin tallafawa jihohin da suke da yawan yaran da basu makaranta

- Irin wadannan tallafin na kudi ga UBEC na jihohi da TETF ga jami'o'i zai tallafawa ilimi

UBE zata raba N150b ga jihohi don ilimi kyauta - Ministan Ilimi

UBE zata raba N150b ga jihohi don ilimi kyauta - Ministan Ilimi

UBEC zata raba Naira biliyan 142.58 domin tallafawa bunkasar ilimi a duk jihohin kasar nan inji Ministan ilimi, Malam Adamu Adamu.

Ya sanar da hakan a taron kwana biyu da akayi a Kaduna na shugabannin gargajiya na arewa akan yaran da suka bar makaranta.

Yace bankin duniya ya samar da kayan dala miliyan 611 rance tsakanin 2016 zuwa yanzu domin tallafawa jihohin da suke da yara mafi yawa da suka bar makarantar a kasar.

"Irin wannan tallafin na UBEC da TETF da ire iren su zasu tallafa gurin habaka ilimi a kasar," inji shi.

DUBA WANNAN: Me kayi da N13Tr a 2015-2018? - Atiku ga Buhari

Adamu yayi kira ga masu ruwa da tsaki akan su hada hannu da karfe domin magance abinda yasa yara ke barin makaranta.

"Dole ne mu ba wa yaranmu ilimin da suke bukata da sana'o'in hannu domin su kawo cigaba ga kasar mu baki daya,"

Ministan yayi godiya ga masarautan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki domin zuwan da sukayi wajen hada karfi da karfe gurin kawo karshen matsalar ilimi a kasar.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel