Obasanjo ya bayyana muhimman dalilai 5 da suka sa ya gafarta ma Atiku gabanin zaben 2019

Obasanjo ya bayyana muhimman dalilai 5 da suka sa ya gafarta ma Atiku gabanin zaben 2019

Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana dalilin da yasa shi ya hakura da duk laifukan da tsohon mataimakin Atiku Abubakar ya tafka masa a baya, da yasa a yanzu ya gafarta masa, kuma ma yake goyon bayan takararsa ta zama shugaban kasa.

Obasaanjo ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, 11 ga watan Oktoba, a yayin ziyarar da Atiku ya kai masa ziyara har gida inda suka ci abincin rana tare, sa’annan daga bisani shehin Malam Dakta Ahmad Abubakar Mahmud Gumi tare da wasu manyan fastoci suka isheshi a gidan na Obasanjo.

KU KARANTA: Takarar gwamna: PDP ta tsayar da Takai a Kano, ta yi watsi da surukin Kwankwaso

A jawabinsa, Obasanjo ya lissafa manyan dalilai da suka sanya ya zama wajibi a gareshi ya gafarta ma tsohon abokin siyasar tasa, inda yace a yanzu ya fahimci Atiku ya sauya halayensa ba kamar yadd yake a baya ba.

Obasanjo ya bayyana muhimman dalilai 5 da suka sa ya gafarta ma Atiku gabanin zaben 2019

Ziyarar

“Zan fara da taya shugabansa mai jiran gado Atiku Abubakar murnar lashe zaben fidda gwani na takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, kuma na ji dadin yadda ya bani girma a cikin jawabinsa bayan ya samu nasarar zaben.

“Maganar gaskiya itace Atiku Abubakar ya gyara halayensa da takunsa, tabbas Atiku ya yi nadamar abubuwan da yayi a baya, kuma ka nemi gafarata, sa’annan ka koyi darussa daga abubuwan da suka faru a baya, bugu da kari za ka gyara alakarka da jama’a tare da gyara kurarakuran baya.” Inji Obasanjo.

Obasanjo ya cigaba da cewa: “Don haka, a matsayina na kirista wanda yake neman gafara game da lafukansa, nima na yafe maka duk abinda ka yi min, na yafe maka kuma ina baka shawarar ka dauki darasi, kuma ka yi abinda ya kamata.”

Daga karshe Obasanjo ya bukaci Atiku ya nema sauran abokan takararsa da ya kayar a zaben fidda gwani na PDP, domin su yi aiki tare a yakin neman zabensa, sa’annan ya bayyana masa idan akwai taimakon da yak enema daga gareshi ya fada masa, ba zai hana shi ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel