Zaben 2019: Darasi 5 da ganawar Obasanjo da Atiku za ta koyar

Zaben 2019: Darasi 5 da ganawar Obasanjo da Atiku za ta koyar

- Obasanjo na da yakinin cewa Atiku ne zai lashe zaben shugaban kasa a 2019

- Obasanjo ya gafartawa Atiku dukkanin laifukan da ya yi masa

- Atiku ya mallaki dukkanin matakan shugabanci da wayewar zama shugaban kasar Nigeria idan aka hadasa da sauran 'yan takara

A yau Alhamis 11 ga watan Oktoba ne dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP ya kaiwa tsohon shugaban kasar Nigeria kuma jigo a jam'iyyar Olusegun Obasanjo ziyara a garin Abeokuta.

A yayin wannan ziyarar, tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo, ya gabatar da jawabai, daga cikin jawab nasa akwai muhimman darasoshi 5 da 'yan siyasa zasu koya, musamman a yanzu da kasar ke fuskantar babban zaben 2019 da ke gabatowa.

KARANTA WANNAN: Amfani da rubabben tumatur na haifar da ciwon daji - NAFDAC ta gargadi jama'a

Zaben 2019: Darasi 5 da ganawar Obasanjo da Atiku za ta koyar

Zaben 2019: Darasi 5 da ganawar Obasanjo da Atiku za ta koyar

1. Obasanjo na da yakinin cewa Atiku ne zai lashe zaben shugaban kasa a 2019.

"Bari na fara da taya mai jiran gadon shugabancin Nigeria, Atiku Abubakar murna, na samun nasarar lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP wanda na nazarci muhimman abubuwan da ya fada a jawabin godiyarsa."

2. Atiku ya yi nadama tare da gane kura kuransa, a cewar Obasanjo.

"Haka zalika ga dukkan matakan nazari, tsohon shugaban kasar ya gane kura kuran da ya aikata kuma a yanzu ya yi nadama. Kamar yadda na sha fada, ba wai kayi mun wasu tarin laifuka bane, kawai dai yadda ka dauki jam'iyyarmu, gwamnati da kuma kasar ne ya saba nawa ra'ayin.

Daga irin abubuwan da suka faru a cikin 'yan awannin nan, ka nuna nadamarka, ka kuma roki gafarata, ko a hakan na san cewa ka koyi darasi da zai hanaka aikata irin hakan a nan gaba, kuma da fatan zaka yi gaggawar gyara tafiyarka."

3. Obasanjo ya gafartawa Atiku

"Bari na sanar maka da cewa, a matsayina na kirista wanda ke rokon gafarar ubangiji idan na yi masa laifi a kowace rana,na gafarta maka dukkanin laifukan da kayi mun har cikin zuciyata, kuma ina shawartarka da ka tuna baya don gina kyakkyawar gaba, komai zai zo maka cikin nasara."

Zaben 2019: Darasi 5 da ganawar Obasanjo da Atiku za ta koyar

Zaben 2019: Darasi 5 da ganawar Obasanjo da Atiku za ta koyar

4. Obasanjo a shirye yake ya tsayawa Atiku don ganin ya lashe zaben 2019

"Har yanzu akwai sauran aiki a gaba, walau a nan cikin kasa ko a wajen kasa, wurare da dama da ya kamata ka katange da kuma dinke barakarka. Zaka iya gane yadda zaka fuskanci abubuwanda suka bayyana fili dama wadanda suke boye a zukatan abokan hamayya. Sai dai ina mai tabbatar maka cewa, idan har ka dore da halin dattako da ka zo da shi a nan, zan tsaya maka tsayin daka, in shiga dakai duk inda ake shiga don ganin ka samu nasara da yardar ubangiji."

5. Atiku ya mallaki dukkanin matakan shugabanci da wayewar zama shugaban kasar Nigeria idan aka hadasa da sauran 'yan takara

"A nawa bangaren, kuma ga dukkanin yan takarar jam'iyyar PDP, kai ne wanda ya cancanci zama dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar, saboda ka mallaki dukkanin kayan aiki da kwarewar ta shugabanci. Daga dan kadan da na sani game da kai, kana da karfin aiwatar da abubuwan da shugaban yanzu ya gaza aiwatarwa.”

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel