2019: Obasanjo ya yafewa Atiku, ya goyi bayan takarar sa

2019: Obasanjo ya yafewa Atiku, ya goyi bayan takarar sa

- Tsohon shugaban kasa, Olusegun Ibasanjo, ya goyi bayan takarar tsohon mataimakinsa, Atiku Abubakar, a zaben shekarar 2019

- Atiku tare da rakiyar wasu manyan malaman addinin Islama da Kirista sun ziyarci Obasanjo a gidansa dake Abeokuta, babban birnin jihar Ogun

- Duk da ya goyi bayan takarar Atiku, Obasanjo bai bayyana cewar ya koma jam'iyyar PDP ba ko kuma zai fito ya yiwa Atiku yakin neman zabe ba

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Ibasanjo, ya goyi bayan takarar tsohon mataimakinsa, Atiku Abubakar, a zaben shekarar 2019.

Obasanjo ya bayyana hakan ne a yau, Alhamis, bayan ya karbi bakuncin Atiku tare da rakiyar wasu manyan malaman addinin Islama da Kirista a gidansa dake Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

A shekarar 1999 ne Obasanjo ya zabi Atiku ya zama mataimakinsa bayan ya ci zabe a matsayin shugaban kasar Najeriya na farar hula a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, kafin daga bisani a sake zabar su a karo na biyu a shekarar 2003.

Sai dai dangantaka ta yi tsami a tsakaninsu gabanin karshen zangon mulkinsu na biyu, da ya kare a shekarar 2007.

2019: Obasanjo ya yafewa Atiku, ya goyi bayan takarar sa

Ziyara Atiku da manyan malaman addini a gidan Obasanjo

A shekarar 2007, Atiku Abubakar ya tsaya takarar shugaban kasa a jam'iyyar ACN bayan Obasanjo ya ki mara masa baya ya samu takara a jam'iyyar PDP.

Tun bayan wannan lokaci Obasanjo ya cigaba da nuna adawar sa ga kudirin Atiku na son zama shugaban kasar Najeriya a duk lokutan da ya yi takara; a 2010 da 2014.

DUBA WANNAN: Atiku da Buhari Danjuma ne da Danjummai - Tsohuwar ministar PDP

Batun goyon bayan takarar Atiku da Obasanjo ya yi, ya matukar bawa jama'a mamaki domin kuwa babu wanda ya yi tsammani hakan. Hasali ma tun a shekarar 2014 Obasanjo ya kira taron 'yan jarida tare da yaga katinsa na zama mamba a jam'iyyar PDP.

Shi kansa Atiku komawa jam'iyyar APC ya yi, in da ya shafe tsawon shekaru uku kafin daga bisani ya kara komawa jam'iyyar PDP a shekarar 2018.

Duk da ya goyi bayan takarar Atiku, Obasanjo bai bayyana cewar ya koma jam'iyyar PDP ba ko kuma zai fito ya yiwa Atiku yakin neman zabe ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel