Saukar ruwan sama mai tsanani ta yi awon gaba da wani 'Dalibi dan shekara 11 a jihar Calabar

Saukar ruwan sama mai tsanani ta yi awon gaba da wani 'Dalibi dan shekara 11 a jihar Calabar

Wani dalibin makarantar Sakandire dan shekara 11, Victor Charles, ya yi gamo da ajali yayin da ambaliyar ruwa ta kwarare shi ta magudanan ruwa a sanadiyar saukar ruwan sama mai tsananin gaske a birnin Calabar na jihar Cross River.

Rahotanni kamar yadda shafin jaridar The Punch ta ruwaito sun bayyana cewa, saukar ruwan sama mai tsananin gaske ta yi sanadiyar kwarare wannan Yaro ta babbar magudanar ruwa dake hanyar Mayne a garin Atakpa dake birnin na Calabar.

Wannan ibitila'i da ya auku a ranar Talatar da ta gabata sakamakon saukar ruwan sama mai tsananin gaske har na tsawon sama da sa'o'i biyu ya jefa al'ummar yankin cikin dimuwa yayin da aka gaza tsinto koda gawar sa.

Saukar ruwan sama mai tsanani ta yi awon gaba da wani 'Dalibi dan shekara 11 a jihar Calabar

Saukar ruwan sama mai tsanani ta yi awon gaba da wani 'Dalibi dan shekara 11 a jihar Calabar

Wani mashaidin wannan lamari, Umana Okoro, ya bayyana cewa tsautsayin ya auku ne a yayin da Victor ke kan hanyarsa ta dawowa daga makaranta tare da wasu abokanan sa biyu.

KARANTA KUMA: An kashe soja guda, anyi garkuwa da wata Mata a jihar Filato

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan lamari ya jefa Malamai da kuma Dalibai cikin damuwa da halin kaico yayin dangane da yadda ajali ya katse hanzarin Victor yana da kananun shekaru.

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, jam'iyyar PDP ta kasa ta yiwa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso tumbur dangane da dan takarar gwamnan jihar da ya tsayar, Abba K. Yusuf.

Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel