Tattalin Afrika ta Kudu, Angola da Najeriya zai noke – Hukumar IMF

Tattalin Afrika ta Kudu, Angola da Najeriya zai noke – Hukumar IMF

- IMF tace tattalin arzikin Najeriya ba zai motsa sosai a 2019 ba

- Wannan zai kara kawowa kasar cikas a bangaren tattalin arziki

Hukumar IMF wanda ke ba da lamuni ta Duniya IMF ta bayyana cewa wasu manyan Kasashe a Afrika za su gamu da cikas a bangaren tattalin arziki. Najeriya da Afrika ta Kudu su na cikin wannan kasashe da aka lissafo.

Tattalin Afrika ta Kudu, Angola da Najeriya zai noke – Hukumar IMF

Najeriya na cikin kasashe 3 da za su gamu da cikas a fannin tattali

IMF bayyana cewa harsashen ta sun tabbatar da lallai Kasar Afrika ta Kudu, da Kasar Angola da kuma Najeriya za su gamu da rashin zabura na tattalin arziki a shekara mai zuwa da kuma shekaru masu zuwa nan gaba kadan.

KU KARANTA: Abubuwa za su cigaba da yin garau a Najeriya inji wanda su ka san tattalin arziki

Hukumar IMF a jawabin da ta fitar kwanan nan ta bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya zai mosta ne da maki 1.9% rak a bana. A badi kuma ana sa rai a samu mostawar 2.3% a Najeriya wanda hakan bai kai yadda ake so ba.

Wani babban Jami;in Hukumar da ke Yankin Afrika Milesi Ferretti ya bayyana wannan a makon, Wannan bayani mai ban tsoro dai yana zuwa ne lokacin da wasu Masana ke ganin tattalin Najeriya ya kama hanyar murmurewa.

Kasar Afrika ta Kudu da kuma Angola mai arzikin mai duk da za su gamu da wannan tawaya na tattalin arziki inji IMF. Motsawar da tattalin kasashen za su yi dai ba zai kai har Matasa da sauran jama’a su samu ayyukan yi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel